SHUGABA BUHARI YAYI JIMAMIN RASHIN KWAMISHINAN TARAYYA NA HUKUMAR TARAWA DA RABON ARZIKIN KASA RMAFC

0

SHUGABA BUHARI YAYI JIMAMIN RASHIN KWAMISHINAN TARAYYA NA HUKUMAR TARAWA DA RABON ARZIKIN KASA RMAFC


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna kaduwan zuciya ya mika ta’aziyya zuwa ga Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi bisa rasuwan Hon. Suleiman Kokori Abdul, kwamishinan tarayya mai wakiltan jihar kogi a hukumar tarawa da rabon arzikin kasa ko kuma kudaden shiga na kasa wato (RMAFC).

Shugaban kasa har ila yau ya jajanta wa shugaban hukumar na kasa da kuma membobin hukumar bisa wannan rashin na kwamishinan tarayya. wanda aka rantsar da shi cikin watan Yuni, na shekarar 2019.

kamar yadda ya ke dan siyasa ne wanda ya fara daga gida kuma tsohon dan majalisan wakilai na tarayya wanda ya wakilci mazabar Okebe/Ogori-Magogo a majalisar kasa ta shida daga shekarar (2007 zuwa 2011), Shugaba Buhari ya bada tabbacin cewa Hon. Abdul ya fahimci wuri na sadaukarwa da kuma tausayi cikin gudanar da aiyukan jama’a: kuma wannan ne ya jawo masa sha’awa da kuma girmamawa cikin siyasa a tsakanin mutanen sa.

Shugaban kasa ya shaida irin gudumawa da marigayi kwamishinan tarayya ya bayarwa ma wannan gwamnati zuwa ga shirin wayar da kai kan kudaden shiga daga bangaren da ba na man fetur ba, kuma yayi fatan cewa wannan sadaukarwan sa zuwa wajibi aikin sa zai ci gaba da gudana a hukumar tarawa da raba kudaden shiga na kasa RMAFC.

Shugaba Buhari yace tunanin mu yana tare da iyalin Abdul a wannan lokaci na bakin ciki har kamar yadda yayi Addu’an zuwa ga Allah ubangiji ya gafarta masa wa shi marigayin kuma ya albarkace tare da samun Aljannar Firdausi.

Malam Garba Shehu:
Babban Mai Tallafawa Shugaban kasa A Kafofin Watsa Labarai da Wayar da kan Jama’a.
14 ga watan Nuwamba, 2020.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here