Budaddiyar wasika zuwa ga Shugabannin MOPPAN da AFMAN

0

Budaddiyar wasika zuwa ga Shugabannin

Salam. Ina mai kara mubaya’a ga Shugabannin kungiyoyin shirya fina-finai na Moppan da Afman tare da mambobinsu bisa la’akari da yadda na san wahalhalun da ke cikin Shugabancin jama’a musamman na ma su sana’ar shirya fina-finai, ko shakka babu, Shugabancin ‘yan film na da matukar wahala kasancewar wani irin zama da ake yi na kai da kafa a tsakanin juna.
A masana’antarmu ne za ku taru ku za6i Shugabanni domin su yi muku aiki, amma da an gama za6en sai kowa ya kade rigarsa ya tafi zarafin neman kudinsa ya bar Shugabanni da hakilon yadda za fidda Jaki daga Duma, wato kawai so ake su bushi iska nan take gyara ya samu sai ka ce ma su rufa-ido. Misali, idan Shugabanni sun ce a zo taro, kalilan ne za su halarta, sannan idan an an ce a biya kudin ka’ida (union dues) kowa na kyashin biya, amma idan Shugabanni sun samo dan wani tagomashi to kowa idonsa na kai, a sannan zai bigi kirji ya ce yana da hakki. Allah ya kyauta.

Na dan yi shimfida ne a kan alakar Shugabanni da Mambobinsu a Kannywood, amma ba nan na dosa ba a a, ina so ne na yi tsokaci a kan rayuwar wannan masana’anta ta fuskar alakarmu da hukumomin Gwamnati musamman ma su jibi da tace fina-finai a matakan jihohi da na tarayya. Misali mu a nan Kano an samar da dokokin harkar fina-finai tun kafin a haifi Kannywood, domin kuwa dokokin da ke kunshe a Hukumar Tarihi da al’adun gargajiya ta jihar Kano ma su alaka da shirya wasannin kwaikwayo, aka tace aka yi wa kwaskwarima aka samar da Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano a wajajen shekara ta 2001. A lokacin ne ma zan iya tunawa mu a Kannywood muka mika na mu tsakanin (input) Mai taken ‘Islamization of Film making in Kano state’

A nan ina so ne na yi tsokaci a kan kalubalen da ke akwai na bambance bambance tsakanin wancan zamani da wannan zamani da muke ciki, misali a wancan zamani babu hanyoyin sadarwa na zamani wadanda a kan iya harba film nan take ya bazu a Duniya lokaci kamar kiftawa da Bismillah, maimakon a wancan lokaci akwai linzami mai karfi wanda kan zamo tarnaki wajan fidda fina-finai ko wasu sakwanni da za a aika da su ta hanyoyin sadarwa, hasali ma in ka cire nta, da Ctv Kano, to ba ka da wani gurin da za ka iya nuna fina-finanka, sai daga baya matasan wancan lokaci suka kirkiro kasuwar sayar da fina-finai a kaset kaset (home video) da kuma nunawa a gidan Kallo, amma yanzu fa? Kowa ya san bambancin a bayyane ya ke.

Duk wadannan bayanai na yi su ne domin na yi Kalubale ga Shugabancin Kungiyoyinmu da mu Mambobi cewa lokaci ya yi da dole sai an zauna an sake karanta dokokin Kano state censorship board domin yi musu kwaskwarima, wanda yin hakan ne zai sa a daina sa zare tsakanin ita wannan hukuma da ma su sana’ar film.

Daga cikin abubuwan da nake ganin ya kamata a duba sun hada da:

1. Alakar dokokin shirya fina-finai ta jihar Kano da irin wannan hukuma a matakin kasa, domin kuwa dole a tafi tare tsakanin jiha da tarayya.

2. Dole a dubi sabbin hanyoyin sadarawa na zamani domin a yi musu mahalli a tsaffin dokokin da ake da su musamman ma da naga yanzu hukuma to fara hararar hanyoyin sadarwa irin su ‘You tube’ wadanda a wancan lokaci babu su, yayin da ma su shirya fina-finai ke tsalle su dire bisa tsoron za a dora musu jakar tsaba a kan YouTube din.

3. Dole a samar da sharudda a dokokin tace fina-finai ta jiha wajan zabar Executive secretary na wannan hukuma domin haska fitila ga duk Gwamnatin da za ta zo, domin kada a mayar da wannan kukera ta Executive secretary ta zamo ta siyasa (political) wato ina nufin a mayar da ita ta kwararru (professionals) tare da gindaya matakan da film maker zai taka kafin ya kai ga darewa kan kujerar.

4. Dole a dubi addini duba na adalci ba na san zuciya ba, ta yadda matukar an taba addinin musulunci to ga hukunce hukuncen da za a yi ga wanda ya saba, sai in abin ya ci tira sai a tafi kotu.

5. Dole sai an samar da shinge na hurumin ikon censors board da kungiyoyin film (professional association) domin kada a dinga karo da juna wajan hukunta dan film ko ma film din kansa.

Ni a fahimtata, matukar ba sake duba dokokin film a ka yi ba to haka za a ci gaba da sa toka sa katsi tsakanin Es Es da ake nadawa da ma su shirya film a jihar Kano da ma sauran jihohi, domin kuwa daftarin da ya samar da dokokin (film policy) na bukatar sabuntawa.
Kazalika Babu mai tsayawa a yi wannan aiki sai Jagorancin kungiyoyin film, su ne za su dauki nauyin lauyoyi da kwararua kan harkar film da masana a addinin musulunci wajan duba dokokin, daga nan su mika su ga Majalisar dokoki kuma su tsaya tsayin daka dan tabbatar da an zartar da gyare gyaren. Ku kuma Mambobi dan Allah ku mu ba su hadin kai.

Wassalam

*#Ibrahim Muhammad Mandawari*
Mai-unguwar Mandawari

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here