Gwamnatin zamfara bata mallaki ma’adinai ba na kashin kanta — kwamishinan ma’adinai
Daga Shuaibu Ibrahim Gusau
A yayin da aketa cecekuce kan ma’adinan jihar zamfara, Wanda al’umma suka kasa fahinma,
Kwamishana mai kula da Ma’aikatar ma’adinai, Dakta Nuruddeen Isa ya ce gwamnatin jihar ba ta mallaki wani fili na kashin kanta na zinare ba.
Kwamishinan ya bayyana hakan a lokacin da yake yiwa manema labarai bayani a ofishinsa, ya ce gwamnatin jihar zamfara ba ta tsunduma kai tsaye kan harkar ayyukan hakar ma’adanai ba, kamar yadda manema labarai suke bayyanawa ba .
Ya kara da cewa “gwamnatin jihar ba ta mallaki wani yanki na filin zinare ba a duk fadin jihar kuma ba ta da hannu a ayyukan hakar ma’adinai”, ya ce gwamnatin jihar tana amfani da sayen gwal ne kawai daga haramtattun masu hakar ma’adanan domin hana shigo da kaya daga kasar waje ko sayar da shi ga ‘yan fashi.
Shugaban ya bayyana cewa “Abin da gwamnatin jihar ke yi shi ne ta sayi zinaren don kar ya fada hannun bata gari wadanda su kuma suke sayar da shi a wajen kasar tare da sayen makamai ga ‘yan fashin”.
Ya ce gwamnatin jihar a halin yanzu ta haramta ayyukan hakar ma’adanai a jihar, “duk wanda yake son shiga harkar ma’adinai to ya samu lasisin daga Gwamnatin Tarayya”, ya ce, albarkatun karkashin kasa na Gwamnatin Tarayya ne, saboda haka, duk wanda yake son shiga aikin hakar ma’adanai dole ne ya samu lasisi daga Gwamnatin Tarayya.