RIKICIN MA’AIKATAN KOTUN KATSINA: MAJALISA TA WANKE AKANTA-JANAR NA JIHA

0

RIKICIN MA’AIKATAN KOTUN KATSINA:
MAJALISA TA WANKE AKANTA-JANAR NA JIHA.

Daga Muazu Hassan
@ Katsina City News

Wani rikici da ya nemi tashi tsakanin kungiyar Ma’aikatan Kotunan Katsina (JUSUN) da gwamnatin na Katsina a kan dakatar da albashin wasu ma’aikata, yanzu ya zo karshe, a inda wani kwamitin da Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta kafa ta gano a binciken ta cewa, ofishin Akanta-janar, Alhaji Malik Anas bai yi wani kuskure ba a matakin da ya dauka.

A ranar 30 ga watan Yuni, Kungiyar Ma’aikatan Kotunan Jihar Katsina (JASUN), ta rubuta wata wasika ga Majalisar Dokokin Jihar tana neman su shiga tsakani a kan wasu ma’aikata su 152 da aka dakatar da biyan su albashi, wasu wata biyu wasu wata 4.

Kungiyar ta yi barazanar cewa, in ba a warware matsalar ba, ba su da wani zabin da ya wuce su fada yajin aikin da zai tsayar da ayyukan kotunan Jihar cak.

Majalisar ta amshi koken, kuma ta kafa kwamiti mai mutane 10 da ya hada ‘yan majalisu guda uku; Hon. Lawal Yaro, Hon. Musa Nuhu Gafiya. Hon. Mustafa Rabe Musa. Sai Wakila daga Babbar Kotun Katsina, Mustafa Hassan Ruma. Sai Wakilai daga Hukumar Shari’ a ta Jiha (JSC), Ibrahim Isiyaku Mashi.

Sauran sune Wakilai daga ofishin Akanta-janar na Jiha, Usman Shehu da Yusuf Abdulsalam. Sai Wakilan kungiyar ma’aikatan kotu, Yusuf Abdul da Yusufu Sani da sakatarensu Falalu Ahmad.

An ba su aikin su gano gaskiyar lamarin ta hanyar tantancewa a kan madogara kamar haka; takardun daukar ma’aikatan aikin, yadda aka dauke su aikin, ganin wadanda aka dauka ido da ido, tabbatar da suna zuwa aikin, yadda aka biyan su albashin baya da yin tambayoyi ga wadanda abin ya shafa da wadanda za su iya ba da bayanin da ake nema.

Kwamitin ya gano cewa a shekarar 2014 an ba da izinin a dauki ma’aikata 114, amma aka dauki 161. A shekarar 2017 an dauki ma’aikata 204 maimakon 132 da aka ba da iznin a dauka.

Kwamitin ya gano an rika daukar ma’aikata ba bisa ka’ida ba da kuma bin ka’ida wajen tabbatar da su, ya kuma gano daukar ma’aikatan da aka yi a 2014 ba a bi ka’ida ba.

Kazalika Kwamitin ya gano cewa an yi wa wasu daraktoci biyu da ke bangaren kudi karin girma ba bisa ka’ida ba, wanda Hukumar kula da aikin shari’a ta yi.

Ya gano an saka ma’aikatan aikin kotun 148 cikin tsarin biyan albashi na Jiha ba bisa ka’ ida ba.

An kuma gano wasu ma’aikata guda tara da aka dauko su daga Hukumar kula da ma’aikatan Kananan Hukumomi zuwa Hukumar kula da ma’aikatan shari’a.

Kwamitin ya ba da shawarar Hukumar kula da shari’a ta Jihar Katsina, ta canza da sake fasalin sashen kudi da gudanarwa ta manyan kotunan Jihar.

Kwamitin ya yi kira da a ladabtar da wadanda aka samu da laifin sako ma’aikatan ba bisa ka’ida ba.

Kwamitin ya yi kira da wadannan daraktocin da aka kara wa girma ba bisa ka’ida ba a sake lale a matsayin da aka ba su.

Kwamitin ya ba da shawarar Hukumar kula da aikin shari’a na Jihar Katsina ya je ya yi nazari a kan ma’aikatan nan 148 da suka dauka ba bisa ka’ida ba.

Kwamitin ya amince da cewa ma’aikatan da aka dauka a 2014 guda 47 ba bisa ka’ida aka dauke su ba.

Sai dai sun gano ma’aikatan san aikin a yanzu sun goge, an kuma horas da su, don haka ana iya kyale su su ci gaba da aikinsu maimakon a yi asarar su ko a dauki wasu da sai an horas da su.

Dukkanin membobin Kwamitin sun amince da sakamako da matsayar da rahoton ya dauka, kuma duk sun saka hannu a karshen takardar rahoton.
A zaman majalisar na ranar 18/11/2020 sun karanta cikakken rahoton kuma majalisar ta amince da rahoton.wanda kamar ya zama doka a majalisar.


______________________________________________
Katsina city news na bisa shafin yanar gizo na www.katsinacitynews.com da sauran shafukan sada zumunta na yanar gizo. Tana da yar uwa jaridar taskar labarai dake a www.taskarlabarai.com. da kuma ta turanci the links news dake www.thelinksnews.com. duk suna a shafukan sada zumunta.duk sako a aiko ga 07043777779.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here