Samar da ingantaccen Ilimi da aikin yi ga matasa ne zai kawo ƙarshen matsalar tsaro a arewa

0

Samar da ingantaccen Ilimi da aikin yi ga matasa ne zai kawo ƙarshen matsalar tsaro a arewa – Kwankwaso

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Tsohon gwamnan jihar Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, ya bukaci shugabanni a arewacin kasar nan musamman gwamnonin da aka zaba don su mulki jihohi 19 da su maida hankali wajen shawo kan matsalar ilimi da samar da ayyukan yi ga matasa.

Kwankwaso wanda kuma mamba ne a majalisar dattawa ta takwas, ya yi wannan kira ne a lokacin da ke ganawa da ‘yan jarida kan al’amarin kasa jiya a Abuja.

Sanatan ya nuna matukar damuwarsa kan yawaitar matsalolin tsaro musamman na ‘yan bindiga, garkuwa da mutane, fashi da makami da suka addabi yankin, yana mai cewa wannan kiran ya zama tilas ne domin lalubo bakin zaren magance matsalar tsaro da ya addabi yankin a halin yanzu.

Ya kara da cewa “Akwai bukatar gaggawa ga shugabanni a arewa musamman zababbun gwamnoni shiyyar da su tashi tsaye wajen magance matsalar samar da ingantaccen ilimi da kuma samar da ayyukan yi ga matasa.

“Lokacin da muke da yawan matasan da ba su da ilimi, ba su da wani aikin yi na tsayuwa da kafafu da zai sanya su bar gagaranba a kan hanya, to kuwa dole za a samu matsala, matsalar kuwa ga ta nan don kowa ya ga halin da matsalar tsaro da ake ciki musamman a arewa,” ya shaida.

Tsohon ministan yana mai cewa matsalar da kasar nan musamman arewa ke fuskanta na tsaro na kara kamari ne a sakamakon wadannan manyan matsalolin biyu, yana mai cewa dole ne fa a tashi a magance matsalar ilimi da samar da ayyukan yi ga matasa muddin ana son shawo kan matsalolin da suka dabaibaye harkar tsaro.

Leadership ta ruwaito gwamnan Yana jaddada cewa muddin babu wadattun tsare-tsaren kyautata ilimi to fa matasa za su samu kansu a cikin duhun kai da jahilci wanda hakan ka iya jefa al’umma cikin matsalar tsaro kamar wanda ake fuskanta a halin yanzu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here