Gwamnatin Tarayya za ta mallaki Kadada dubu 720,000 a kowace jiha don aikin gonaaa

0

Gwamnatin Tarayya za ta mallaki Kadada dubu 720,000 a kowace jiha don aikin gona — Sabo Nanono

Daga Ibrahim Hamisu

Gwamnatin tarayya ta ce tana kokarin mallakar sama da kadada dubu 720,000 daga jihohi daban-daban don inganta amfanin gona,

Ministan Noma da Raya Karkara, Alh. Sabo Nanono ne ya bayyana haka a jiya Alhamis a wata ganawa da ya yi da shugabannin gudanarwa na maaikatu da kuma manyan jami’an gudanarwa na Ma’aikatar aikin Gona ta tarayya da raya Karkara a Abuja.

Ya ce ma’aikatarsa ​​ta tanadin fili tsakanin kadada dubu 20 zuwa 100,000 a kowace jiha da nufin bunkasa bangaren noman kasar nan. Gwamnatin Tarayya za ta mallaki kadada dubu 720,000 daga dukkan jihohin 36.

Ministan ya kara da cewa “A yanzu haka, ma’aikatar ta dauki kwararan matakai na sanya tsarin binciken aikin gona, da samar da kadada dubu 20 zuwa 100,000 a kowace jiha don amfanin aikin gona, da kuma inganta ayyukan gona da hadin kai a duk ƙasar.
“Tsammani mu shine tura ingantattun iri, fadada yankin noma da tallafawa ayyukan noma a kasar.”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here