Muna Nan Daram-dam A Jam’iyyar PDP, Cewar Gwamna Tambuwal
Daga: Abdulhakim Muktar
Gwamnonin da aka zaba a karkashin jam’iyyar PDP, sun sake nanata biyayyar su da jajircewa wajen ƙarfafa jam’iyyar.
Shugaban kungiyar gwamnonin PDP, Aminu Waziri Tambuwal, ya yi magana a madadin takwarorinsa a taron NEC na 90 na jam’iyyar da ke gudana a sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa, Wadata House, Abuja.
“Dukkan mu 15 muna nan, kowane ɗayanmu ya himmatu ga kyakkyawan shugabanci a jihohinmu daban-daban domin ƙarfafa jam’iyyarmu”. Inji Tambuwal.