Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Bukatar Kungiyar ASUU

0

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Bukatar Kungiyar ASUU

Daga Ibrahim Hamisu

Gwamnatin tarayya a yau Juma’a ta amince cewa za’a cire mambobin kungiyar ASUU daga tsarin biyan albashi na IPPIS.

A sanarwar bayan taro da ministan Kwadago, Chris Ngige ya fitar ta ce, gwamnati ta amince da bukatar kungiyar ASUU na biyan albashin mambobin kungiyar na watan Fabarairu zuwa Yuni ta kan tsohon tsarin GIFIMS.

Haka kuma gwamnatin ta bada damar kara yawan biyan alawus din da kungiyar ta ke bi daga Naira Biliyan 30 zuwa Biliyan 35 da kuma kara kudin gyararrakin jami’o’i daga Naira Biliyan 20 zuwa biliyan 25.

An dai dade ana kai ruwa rana tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar ASSU akan tsarin biyan albashin malaman jamia na IPPIS.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here