AN KAI HARI GIDAN DAN MAJALISAR TARAYYA YAHAYA KUSADA

0

AN KAI HARI GIDAN DAN MAJALISAR TARAYYA YAHAYA KUSADA
muazu hassan
@ katsina city news
A daren jiya asabar 21/11/2020 da misalin karfe daya na dare wadansu mahara da ba a San ko su waye ba.suka kai Hari gidan Dan majalisar tarayya mai wakiltar kusada,kankia da ingawa da ke jahar katsina ,
Maharan da ba san adadin yawansu ba. Sun kai harin ne a gidan Dan majalisar dake garin kusada karamar hukumar kusada a jahar katsina.
Maharan sun tafi da ma aikatan gidan biyu wata mata mai suna Talatu da wani matashi mai suna Suleman.
An tabbatar mana da cewa, an sanar da jami an tsaro kuma sun je gidan sun dau bayanan abin da ya faru.
Mun kuma samu labarin a daren jiya, wasu maharan sunyi ma wasu yan sa kai a karamar hukumar kurfi kofar raggo suka halaka uku daga cikin su.
Mun samu labarin cewadaukin da jami an tsaro suka kai cikin gaggawa shine ya rage barnar wadanda akayi ma kofar ragon.
________________________________________________
Katsina city news na a bisa yanar gizo na www.katsinacitynews.com da bisa shafin Facebook page .Facebook group. Twitter, Instagram , you tube TV da sauran shafukan sada zumunta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here