Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Gwamna Masari, Nusarwa game da Sabuwar Annoba A Katsina.
Daga
Rabiu Na’auwa Balarabe
naauwa1@gmail.com
Ya Maigirma Gwamnana ina fatan wannan wasika tawa ta sameka cikin aminci da kyakkawan fatan zata samun duba daga gareka.
Maigirma Gwamana na zabi rubuta maka wannan wasika ne saboda ina ganin ita ce hanyar sadar da sakona mafi sauki zuwa gareka.
(Aminu amin Talaka) Kamar yanda na ji wani kirarinka a bakuna daban-daban, to in kuwa haka ne amininka talakan jihar Katsina yana cikin wani hali wanda ya dace a dubeshi da idon rahama.
Ya Maigirma Gwamna nasan baka da masaniyar irin annobar da ta kunno kai a jiharka ta Katsina, haka kuma mutanen dake kusa da kai basu sanar da kai ba, watakila ko don hakan bai damesu ba saboda suna da mafita su da iyalansu, ko kuma daular da suke ciki bata barsu sun san halin da aminanka Talakawa da suka loda maka kuri’ unsu tare da amanar kawunasu ta hanyar Jagoranci suke ciki ba.
Ya Maigirma Gwamna ko kasan annobar zazzabin cizon sauro ta rikewa al’umar Jihar Katsina wuya? Nasan za ka ce lokaci ne, ko kayi tunanin menene sauro balle tasirinsa, to babu shakka gindin zama da sauro ya samu a jiharka ta Katsina shi ne sanadiyyar wannan annoba, kuma babu shakka Talakawanka suna shan wuyar wannan annoba musamman in muka yi la’akari da yanayin da ake ciki na hauhawar farashin kayayyaki, ga kuma karancin samayya.
Ya Maigirma Gwamna dame talakanka zai ji? Neman abincin da zai ci ko tsadar magani wanda in ma ya sha ya dan samu sauki, shi sauron kullun kara hayyafa yake saboda babu wani mataki da gwamnati ta daukar masa.
Maigirma Gwamana in har zaka tuna gwamnatocin baya da suka gabata duk bayan yan kwanaki suna kewaye jihar Katsina da feshin maganin sauro wanda hakan yana da tasiri matuka wajan kashe kaifin yaduwar wannan annoba. Haka kuma, a yanzu haka mafi yawan Jihoshin da suke makwabtaka damu suna wannan feshi akai- akai wanda hakan ya sa jama’arsu sun samu saukin wannan annoba, amma mu a nan Katsina shiru kake ji duk kuwa da cewa akwai Hukuma ta musamman dake kula da wannan al’amari.
Ya Maigirma Gwamana ka dubi talakan jihar Katsina da idon rahama, wallahi wannan annoba ta ta’azzara, yakamata a bar talaka ya ji da abincin da zai ci, wahalar nemansa da tsadar kayan masarufi. Hakika da hukuma zata dawo da wannan feshi da muke gani a makwabta ba shakka zamu samu saukin wannan annoba.
A iya sanina Gwamna mutum ne mai jin koken talakawansa, muna roko a dubi talakan jihar Katsina da idon basira.
A karshe ina yi maka fatan alkhairi, ina roka maka Allah ya baka ikon sauke nauyin dake kanka na al’umar jihar Katsina. Bissalam