Mu bamu janye yajin aikin da mu ke ba – ASUU

0

Mu bamu janye yajin aikin da mu ke ba – ASUU

Daga Ibrahim Hamisu

Ƙungiyar malaman jami’o’in ta ƙasa wato ASUU ta yi watsi da rahoton cewa ta janye daga yajin aiki da ta ke kan yi.

Shugaban kungiyar ta ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemii, ne ya bayyana haka a jiya Asabar, inda ya ce har yanzu yajin aikin watanni takwas da su ke yi ya na nan daram dam.

Tun da farko Farfesa Biodun Ogunyemi ya karyata rahotonnin da ke cewa ASUU ta janye daga yajin aiki kuma ya jaddada cewa ASUU ba ta da shafin Tuwita.

“Ƙungiyar ASUU ba ta da shafi a Tuwita. Mutane da dama suna damu na da kiraye-kirayen waya kuma na gaji”

See also  Mai Martaba Muhammad Sanusi II, Sarkin Kano na 14, ya sauka a Oxford,

Kungiyar ASUU ta fara yajin aikin ne tun a cikin watan Maris tun kafin bullar cutar Korona a Najeriya.

Daliban da iyayensu da sauran masu ruwa da tsaki a Najeriya sun kagu da ganin an warware matsalolin da su ka dabaibaye lamarin jami’o’in kasar nan ko za a samu su cigaba da karatu kamar yadda yayan manyan jami’an gwamnati da masu hannu da shuni su ke yi a jami’o’i masu zaman kansu da na kasashen waje.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here