Shigar yara mata makarantu a matsayin abin karfafa

0

Shigar yara mata makarantu a matsayin abin karfafa —- HILWA

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Ganin yadda ake barin yara mata a kan bangaren ilimi a baya,wata kungiya mai zaman kanta mai suna (HILWA) ta bayyana karuwar shigar yara mata a makarantu boko a matsayin abin karfafawa.

Shugabar kungiyar, ta (HILWA) Misis Azuka Menkiti ta bayyana haka a lokacin rufe taron kungiyarta ta Kasa da aka gudanar a Gusau, ya ce HILWA ita ce kan gaba a kamfen din don karfafa yawan shigar da yara mata musamman a Arewa, tare da yin duk mai yiwuwa don hana iyaye tura yaransu yawon barace-barace.

Shugaban kungiyar taci gaba da cewa kungiyar ta( HILWA ))tare da hadin gwiwar UNICEF da Hukumar Kula da Ilimin Firamare ta Jihar Zamfara sun yi nasarar kamfen din kara yawan shigar yara mata da kuma samun ingantacciyar hanya.

Da take tofa albarkarkacin bakinta a wurin taron ,Shugaban kungiyar reshen jihar kano , farfesa A’isha Abdu Isma’il, ta bukachi a ba mata kaso 35 daga chikin dari a wajen zartaswa a bangaren ilmi sakamakon ganin yadda mata ke taka matukar rawan ganin a harkar ilimi a kasannan.

HILWA ta kuma jinjinawa hukumar ilimin ta jihar zamfara musamman kan dabarun samar da ilimi ga yara mata, wanda Gwamna Bello Mohammed Matawalle ya gabatar a matsayin abin birgewa.

Ta ce”Kungiyarmu ta gamsu da matakin da aka samu na shigar da yara mata a makarantun gwamnati don inganta damar samun ingantaccen ilimi” .

Shugaban hukumar kula da ilimi na bai-daya na jihar Zamfara (ZSUBEB), Alhaji Abubakar Aliyu Maradun a nasa jawabin a wurin taron ya ce kwamitin sun tashi tsaye wajen ganin an samar da yanayi mai kyau na koyarwa da ilmantarwa domin karfafawa yara kanana shiga makaranta.

Domin karfafa guiwan wadanda suke taka rawan ganin wajan ganin kungiyar ta tsayu da kafafunta , don ganin kwalliya ta biya kudin sabulu, ayayin da kungiyar ta karrama wadansu mutane ciki harda mai maimartaba Sarkin Musulmi , Alhaji Saad Abubakar, da Sarkin Argungu Alhaji Muhammad Mera da Sarki Anka Alhaji Attahiru Ahmed da tsohon Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi kyaututtuka.

Sauran wadanda suka samu irin wannan lambar yabon sune matar tsohon gwamnan jihar Bauchi Hadiza Mohammed Abubakar, matar gwamnan jihar Sakkwato Mariya Aminu Waziri Tambuwal da matar gwamnan jihar Kebbi Dr Zainab Shinkafi da sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here