Zamfara: ‘Yan Bindiga Sun Ɗauke Limami Da Mamu 30 A Masallacin Juma’a

0

Zamfara: ‘Yan Bindiga Sun Ɗauke Limami Da Mamu 30 A Masallacin Juma’a

November 21, 2020
Ibrahim Ammani

Rahotanni daga jihar Zamfara sun bayyana cewar ‘yan ta’adda masu Garukwa da mutane sun shiga garin Kanoma dake karamar hukumar Maru ta jahar Zamfara a jiya juma’a dai dai lokacin da ake gabatar da sallar juma’a suka tafi da mutane 30 cikin har da Limamin garin na Kanoma.

Lamarin satar jama’a a yankin Arewacin Najeriya na ƙara ɗaukar sabon salo, inda a kusan kullum ‘yan Bindiga ke kai farmaki akan jama’a su kashe na kashewa su kama na kamawa sannan su nemi kuɗaɗen fansa.

Gwamnatocin Jihohin Zamfara da Katsina inda Bala’in ‘yan Bindigar ya fi tu’azzara sun ɗauki matakai a baya na yin sulhu da ‘yan Bindiga amma buƙata ba ta biya ba, maimakon biyan buƙata sai abubuwa suka ƙara dagulewa.

See also  Boko Haram ta kashe sojojin Najeriya yayin wani sabon hari a Borno.

Hakika akwai tashin hankali ace irin taron ranar juma’a dan ta’adda ya ratsa masallacin juma’a ya tafi da Limami da sauran jama’a.

Allah ya kawo mana karshen wannan bala’i.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here