WANI ABU DA BAKU SANI BA GAME DA RAYUWAR MUTANE A ZAMFARA.

0

WANI ABU DA BAKU SANI BA GAME DA RAYUWAR MUTANE A ZAMFARA.

Aliyu Samba

Na ziyarci wani kauye dake karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara da ake kira Bagega, kauye ne da yake da adadi mai yawa na yara kanana da tsofaffi masu shekaru. A tattaunawar mu da sashen mazauna garin, sun bayyana mana irin matsanancin hali da suke ciki sakamakon yan bindiga da suke makotaka dasu, sukan shigo kusan kullum su dauki mutane mazan su da matan su suyi daji dasu. Mafi munin lamarin shine, idan suka tafi da su ba kudi suke nema ba, fyade suke wa mazan su da matansu. Idan wani ko wata yayi gardama sai su kashe su.

Yaran su kanana suna fama da wata iriyar cuta da take sauya musu halitta, kuma binciken mu ya nuna cewa hakan ya faru ne sakamakon abinda ake cewa “Lead Poison” wanda yake kassara sassa jikin dan adam har yayi silar mutuwar sa. A kauyen har ka fita bazaka samu jami’i guda daya ba na tsaro, bazaka samu wani abu na cigaba ba daga “social amenities”, babu ruwa, babu hanya, babu asibiti babu makarantu.

See also  KOWA YA YI FANSHI KANSA DA NAIRA DUBU 50

Gwamnatin Zamfara da gwamnatin tarayya sun gaza matuka akan al’ummar wannan yanki, sun gaza wajen tsare rayukansu da lafiyarsu. Akwai tsohuwa da ta doshi shekaru 60, a bayanan ta take cewa sanda aka sace su aka kaisu, yan bindigar suna zabar matan da zasu yiwa fyade, wani yaro da bai wuce 25 ba yace shi ita yake so, harda cewa wai tsohuwa tafi ****. Cikin kwalla take sheda mana wannan, bayan ita akwai wata da aka harba a mazaunan ta saboda taki yarda ta kusance wanda yake nufin hakan akanta. Lamarin yayi tsanani yayi tsamari, har takai ba kowa zaka cewa zaka je Bagega ba ya yarda kaje, don sunan wajen dead zone kawai a takaice.

Shin babu abinda za a yi kenan dan cetan rayukan mutanen wannan kauye, babu abinda gwamnati zatayi dan gyara wannan barna?
#SecureNorth

©Aliyu Samba
23rd November 2020

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here