Shugaba Buhari na so Sanatoci su ɗaga wa Farfesa Yakubu ƙafa a karo na biyu

0

INEC: Buhari na so Sanatoci su ɗaga wa Farfesa Yakubu ƙafa a karo na biyu


Shugaba Muhammadu Buhari ya buƙaci Majalisar Dattawa da ta amince da zaɓin sa na Farfesa Mahmood Yakubu a matsayin Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) don yin wa’adi na biyu.

A cikin wata wasiƙa da ya aika wa Shugaban majalisar, wato Sanata Ahmad Lawan, wadda aka karanta a zauren majalisar a ranar Talata, Buhari ya ce, “Bisa la’akari da sashe na 154 (ƙaramin sashe na 1) na Kundin Tsarin Mulkin Jamhuriyar Tarayyar Nijeriya (wanda aka gyara), ina farin cikin gabatar wa da Majalisar Dattawa da Farfesa Mahmood Yakubu don a tabbatar masa da yin wa’adi na biyu.”

See also  Kungiyar Fityanul Islam Ta Bayyana Goyon Bayanta Ga Mai Martaba Sarkin Kano

Shugaban Ƙasar ya ce ya na sa ran za “a gaggauta duba” wannan buƙata tasa.

Idan an tuna, kwanan baya ne Buhari a cikin wata sanarwa ya bayyana zaɓen Yakubu domin yin wa’adi na biyu a matsayin Shugaban INEC.

Shi kuma Yakubu, kwanan nan ya ja baya daga shugabancin hukumar saboda wa’adin sa ya cika, ya dakanci Majalisar Dattawa ta sake tabbatar masa da naɗin nasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here