JAMI’AN KWASTAM A KANO SUN KAMA HARAMTATTUN KAYAN MILYAN 24

0

JAMI’AN KWASTAM A KANO SUN KAMA HARAMTATTUN KAYAN MILYAN 24

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Jami’an Hukumar Kwastam ta jihar Kano, ta cafke kayayyakin fasakwauri na naira miliyan 24 a shiyyar kano,

Hukumar yaki da fasakwauri ta kasa shiyyar Kano da Jigawa ta samu nasarar damke kayayyakin fasakwauri da kudinsu ya kai naira miliyan 24,

Shugaban shiyyar na hukumar O.A Olarukoba ne ya bayyana haka ga manema labarai a hedkwatar hukumar da yammacin jiya,

Olarikoba ya ce an kama buhunan shinkafa guda 208, Da dilar Gwanjo guda 268, da Gakangalan din Manja guda 53, sai Katan katan na maganin sauro guda 35, da katan din Sabulu guda 9, da ababin hawa guda 3, da kuma katan din Taliya guda 94.

See also  Uba Ya Sayar Da Dansa Mai Shekara 9 Kan Naira 400,000

Olarikoba dai shi ne ya maye gurbin Nasir Ahmed da akaiwa canjin aiki a hedkwatar hukumar da ke shiyyar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here