Liverpool 0-2 Atalatanta: Liverpool ta yi rashin nasara mafi muni a karkashin Klopp
A karon farko an lallasa kungiyar kwallon kafa ta Liverpool d kwallaye fiye da 1 a gidansu a karkashin mai horaswar Jurgen Klopp. Atalanta ce tawa Liverpool wannan abin kunya a wasan gasar Champions League da suka buga a daren yau.
Wani abin karin daukar hankali a wasan shine Ko sau daya Liverpool bata kai hari me kyau ba.
Ita Kuwa Real Madrid ta yiwa Inter Milan 2-0 ne. Hazad ne ya ci bugu daga kai sai gola yayin da dan wasan Milan, Hakimi, ya ci kungiyarsa bisa kuskure. A baiwa Arturo Vidal jan kati a wasan inda Inter Milan ta kamma wasan da mutane 10.
Bayer Munich ta wa Salzburg 3-1 inda Lewandowski, Coman, da Leroy Sane suka ci kwallaye 1 kowannnsu.