MACIJI YA SARI MAHADI SHEHU

0
426

MACIJI YA SARI MAHADI SHEHU
Muhammad Ahmad
@ jaridar taskar labarai
Wani maciji Wanda ba a San daga inda ya fito ba , ya sari mahadi shehu sanannen mai zarge zargen nan akan gwamnatin katsina da wasu jami anta.
Lamarin ya faru litinin 23/11/2020 ne yau da yamma bayan Mahdi shehu ya kai kansa da kansa a hedkwatar yan sanda ta kasa dake Abuja kamar yadda aka yi dashi a jiya.
Jiya lahadi 22/11/2020. jami an yan sanda sunyi yunkurin kama shi a wani taro da ya halarta a Abuja. amma aka samu fahimtar juna da masu shirya taro da yan sanda da mahadi akan a kyale shi yau ya kai kanshi da kanshi.
A yau 25/11/2020 bayan sun kammala yi masa tambayoyi ance sai ya kebe don ya yi tsarki sai kawai wani maciji ya sare shi. Dan Mahdi shehu mai suna Abba suna a tare a lokacin shine ya fargar da jami an tsaron dake tare dashi cewa .maciji ya sari mahaifinshi.
Ana ganin haka yan sanda suka yi gaggawan kaishi asibitin kasa dake Abuja inda likitoci suka kawo daukin gaggawa suka kula da kafar da macijin ya Sara.
Mahadi shehu yana cikin hayyacin sa kamar yadda majiya ta tabbatar wa da jaridar nan.har ma yayi waya da wasu mutane gaban wasu ciki harda mai bamu labarin.
A dai dai lokacin rubuta labarin nan .Dan sa Abba da wasu jami an yan sanda ke kula da mahadi a asibitin kasa da ke Abuja.
________________________________________________
Jaridar taskar labarai jarida ce mai zaman kanta dake bisa yanar gizo a www.taskarlabarai.com da kuma sauran shafukan sada Zumunta.tana yan uwa sune The links news dake www.thelinksnews.com da kuma katsina city news dake a www.katsinacitynews.com duk sako a aiko ga 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here