MAHADI SHEHU YA KARYATA MACIJI YA SARE SHI, KUMA ‘YAN SANDA SUN KAMA SHI

0

MAHADI SHEHU YA KARYATA MACIJI YA SARE SHI, KUMA ‘YAN SANDA SUN KAMA SHI

Muhammad Ahmad
@ Jaridar Taskar Labarai

Alhaji mahadi Shehu mai kwarmaton zarge-zargen nan ga gwamnatin Katsina a shafin sadarwar zamani da sauran kafofin watsa labarai, ya musanta labarin da jaridar TASKAR LABARAI ta buga cewa wani maciji ya sare shi a ofishin ‘yan sanda a Abuja.

Mintuna kadan bayan fitar labarin, Alhaji Mahdi Shehu, ya aika wa babban Editan jaridar da sakon wayar hannu yana cewa ba a nemi jin ta bakinsa ba kafin a saki labarin.

Ya ce karya ne ba haka labarin yake ba, Yana mai neman a bayyana nasa bangaren na cewa ya karyata, kamar yadda ka’ida da dokar aikin jarida ta nuna.

Da safiyar nan jami’an jaridar sun sake magana da Alhaji Mahadi Shehu, wanda ya yi ikirarin baka da baka cewa, hoton da aka sanya ba nasa bane.

Ya ce shi a gidansa ya kwana, kuma ba wani macijin da ya sare shi.

Ya ce yana da wani shiri da yake yi a Kano a cikin makon nan da ake ciki, kuma zai ci gaba da fallasar da yake yi.

Sai dai Wakilanmu sun kara bin diddigin labarin, inda suka tabbatar da gaskiya ne, Mahadi ya je hedikwatar ‘yan sanda ta kasa da ke Abuja a ranar Larabar da ta gabata.

Kuma tabbas an masa tambayoyi (muna da sunayen ‘yan sandan da suka yi masa tambayoyi da ofishin da ya je da lokacin da ya je).

Tabbas an kai Mahadi Shehu asibiti daga hedikwatar ‘yan sanda ta kasa, mun ga takardun da aka cika da sunansa a kan an kawo shi asibiti ba shi da lafiya (mun gan su
da sunayen ‘yan sandan da suka cika takardun).

Mun saka hoton da muka samu a na’urarmu ta tantance hotuna, sun tabbatar hotunan na Mahadi Shehu ne.

Abin da jaridar ba ta samu rahoton Likita a kan ba shi ne, shin maciji ne ya sare shi?

Shaidun baka sun tabbatar wa da jaridar nam cewa, maciji ya sare shi, amma muna kokarin samun rahoton Likita domin tantancewa da nufin tabbatar da gaskiyar ikirarin.
Muna da tabbacin har yanzun da safe Mahadi yana asibitin kasa dake Abuja.don tabbatar da ingantar lafiya sa.
Muna da tabbacin wasu manyan yan katsina dake Abuja suna ta kokarin cewa an sallame shi daga wajen yan sanda a yau. Mun magana da wasu baka da baka sun tabbatar mana suna wannan kokarin.
________________________________________________
Taskar labarai jarida ce mai zaman kanta dake bisa yanar gizo a www.taskarlabarai.com tana kuma sauran shafukan sada zumunta.07043777775

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here