NA BIYA BILIYAN 1.8 GA DALIBAN DA KWANKWASO YA YI WATSI DA SU

0

NA BIYA BILIYAN 1.8 GA DALIBAN DA KWANKWASO YA YI WATSI DA SU– Gwamna Ganduje

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa ya kashe Biliyan 1.8 wajan daukar nauyin ‘yan jihar zuwa Karatu a Jami’o’i masu zaman kansu a cikin Nijeriya.

Yana mai cewa daliban wanda tsohon gwamnan jihar Rabiu Musa Kwankwaso yayi watsi da su, suna karatu ne a jami’o’in da suka hada da AUN, Crescent University, Al-Qalam University, Bells University of Technology, Otta. Igbinedion University, Okada.

Ganduje ya bayyana hakane yayin mikawa dalibai 20 Shahadar kammala karatunsu.

A jawabinsa kakakin gwamnan Abba Anwar ya ce gwamnatin Kwankwaso ce ta kai wadannan dalibai karatu inda aka yi musu karyar cewa an biya duka kudin karatun amma ba gaskiya bane.

Sai dai yace zuwan Gwamnatin Ganduje sun lura da hakan kuma sun ci gaba da biyan kudin karatun daliban, tunda su ma ‘ya’yansu ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here