Bello Matawalle ya yabawa Gwamna David Umahi da ya fice daga jam’iyyar PDP
Daga Shuaibu Ibrahim Gusau
Gwamna Bello Mohammed (Matawallen Maradun) ya ce
ya yaba wa Gwamnan David Umahi da ya yanke shawararsa na komawa APC maimakon yin Allah wadai da shi, saboda kowa yana jin maraba ne kawai a gidan da yake jin daɗi.
Gwamnan ya bayyana hakane cikin wata takarda mai dauke da sa hannun, mai ba shi shawara na musamman,Zailani Bappa, ya ce “Idan wannan dabi’ar ta haifar da mummunan kin jini a tsakanin mu ya ci gaba ba tare da wani tashin hankali ba, babbar jam’iyyar mu za ta ci gaba da kasancewa cikin rarrabuwar kawuna a yayin da muke tunkarar shekarar 2023,” in ji Gwamna Matawalle.
Ya kara da cewa “Ina fuskantar mummunan yanayi a kwanakin nan daga wasu abokan aiki na Gwamnonin PDP, wanda har yanzu abin na daure kai, musamman , Gwamnonin Kudu-maso-Kudu da ke zargina a kafafen yada labarai.
Ya ce Gwamnoni ne na PDP kuma su mutane ne iri daya da suka haifar da rikici a kan batun Zinaren jihar Zamfara, wanda aka shirya shi a kan karya da gangan da kuma karairayi “. . in ji shi
Abin mamaki shine, Gwamnatin Tarayya ta APC wacce ke da cikakkun bayanai game da batun hakar zinare ,sune suka fito don kare ni a wannan lamarin, duk da zamana na abokan aikin PDP, ina sa ran Gwamnonin za su fara tuntuba ta tukuna don jin nawa bangaren na Labari kafin fitowa kafofin watsa labarai “, ya ce
Bello ya ci gaba da cewa “A yau, Gwamnatin Tarayya tana bayar da lasisi ga Kamfanoni da suka cancanta don yin aiki a bangaren hakar ma’adinai a jihar, ya ce Babban kamfani da ke saka jari na biliyoyin nairori mallakar wani dan Najeriya ne daga jihar Anambra.
Kuma a cewar sa Kamar yadda yake a yanzu, Gwamnatin Jihar ba ta da hannu a duk wani aikin hakar ma’adinai a jihar saboda tsarin mulki bai ba mu ikon yin hakan ba, “in ji Matawalle.