Gwamnan Ondo ya yabi shirye-shiryen rage raɗaɗin rayuwa
Gwamnan Jihar Ondo, Oluwarotimi Odunayo Akeredolu, ya yaba wa Gwamnatin Tarayya kan shirye-shirye daban-daban da ta fito da su don rage wa al’ummar Nijeriya matsalolin rayuwa.
Ya bayyana haka ne a wajen bikin ƙaddamar da shirin musamman na bada tallafin kuɗi ga matan karkara (Special Cash Grant Programme for Rural Women) a Jihar Ondo wanda Gwamnatin Tarayya ke aiwatarwa.
Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ita ce ta ƙaddamar da shirin inda aka agaza wa mata 200 da aka zaɓo daga yankunan ƙananan hukumomi 13 na jihar.
A lokacin da ta ke gabatar da jawabi ga matan a Jihar Ondo, ministar ta yi kira a gare su da su yi amfani da wannan dama da su ka samu wajen inganta hanyar samun kuɗin shiga da hanyoyin samun abincin su, kuma su bada gudunmawar su wajen inganta rayuwar su ta yau da kullum.
Ta ce, “Na yi amanna da cewar tare da goyon bayan mai girma Gwamna, waɗanda za su ci moriyar wannan shiri su na kan hanyar su ta ficewa daga tarkon fatara zuwa ga samun albarka kuma za mu iya ceton ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga ƙangin fatara da yunwa daga yanzu zuwa shekara ta 2030 kamar yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya hango.”
Sadiya Umar Farouq ta kuma bayyana cewa an tsara za a fara biyan kuɗin tallafin kuɗi kai-tsaye a ƙarƙashin shirin nan na ‘Conditional Cash Transfer’ a jihar na watan Satumba zuwa Disamba, 2019 kwanan nan, wanda daga nan za a dakatar da shirin saboda wasu matsaloli da aka samu da tsarin biyan kuɗin, wato ‘Payment Service Provider’ (PSP) da hukumar ICPC.
Ta ce, “Ana nan ana warware wannan matsalar kuma ina tabbatar wa da masu cin moriyar shirin cewa za su ci gaba da amfana da shi gadan-gadan.”
A nasa jawabin, Gwamna Akeredolu ya gode wa Gwamnatin Tarayya saboda shirye-shirye daban-daban da ta fito da su don magance matsalolin rayuwa waɗanda Jihar Ondo ta ke amfana da su, wato irin su ‘Conditional Cash Transfer’, ‘Home Grown School Feeding’, ‘Special Grant Transfer’, da ‘Public Workfare and Skills for Jobs’ a ƙarƙashin shirin tallafa wa matasa.
Gwamnan ya ce shirin bada tallafin kuɗi ga matan karkara wata dama ce ta ƙarfafa wa mata rayuwa, rage fatara da kuma farfaɗo da tattalin arziki bayan da annobar korona ta shafi rayuwar ɗimbin jama’a.
Ya ce, “Al’ummar Jihar Ondo su na miƙa godiyar su ga Gwamnatin Tarayya saboda waɗannan shirye-shirye na inganta rayuwa da su ka sauya rayuwar matan karkara a jihar mu. Da yawa daga cikin waɗannan matan sun tashi daga matsayin masu rayuwar fatara zuwa masu ɗan jin daɗin rayuwa. Su na gudanar da sana’o’in su yanzu a cikin babbar damar faɗaɗa su.
“Gwamnatin Jihar Ondo ta na matuƙar jin daɗin wannan shiri na inganta rayuwar matan karkara a matsayin wata hanya ta rage fatara da yunwa. Wannan shiri ya yi daidai da muradin gwamnatin Jihar Ondo na fitar da yawancin mata daga tarkon fatara. Don haka ne ma gwamnatin a ko yaushe ta ke aiki da shirye-shiryen inganta rayuwa don tabbatar da samar da nagartattun hanyoyin samun sana’a ga talakawa, musamman ma dai mata.”
Gwamna Akeredolu ya kuma yi alƙawarin yin aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin Gwamnatin Tarayya don tabbatar da cewa an samu inganci a rayuwar jama’ar Jihar Ondo, musamnan matan karkara.