MAHADI SHEHU NA HANNUN ‘YAN SANDA

0

MAHADI SHEHU NA HANNUN ‘YAN SANDA

Muhammad Ahmad
@ Jaridar Taskar Labarai

Har zuwa yau Asabar 28/11/2020, Alhaji Mahadi Shehu, sanannen mai kwarmaton nan na zarge-zarge a kan almundahana da yake zargin ana yi a gwamnatin Katsina, yana tsare a wajen ‘yan sanda da ke Abuja.

Mahadi Shehu dan asalin Jihar Katsina ne mazaunin Kaduna , ya kai kansa hedikwatar ‘yan sanda ta kasa da ke Abuja sakamakon gayyatarsa da aka yi a ranar Larabar da ta gabata.

A kuma ranar wani ibtilai ya same shi, na saran maciji, wanda ya karyata da bakinsa ga wannan jaridar. Amma tabbas lamarin ya faru, kamar yadda muka tabbatar.

A ranar Alhamis ya koma Hukumar ‘yan sanda don ci gaba da bincike kamar yadda ‘yan sanda suka ce suna yi a kan zarge-zargen da yake yi wa gwamnatin Katsina.

A ranar Alhamis Mahadi Shehu ya kwana zuwa Juma’a asibitin ‘yan sanda da ke Abuja, bisa la’akari da Hukumar ‘yan sanda ta yi na cewa yace ba shi da lafiya.

A safiyar Juma’a an ci gaba da bincikensa a Hukumar ‘yan sanda ta kasa da ke Abuja, inda ake saka masa bidiyonyin da ya yi don ya tabbatar da nasa ne ko a’ a.

Tun ranar Laraba Lauyoyin Mahadi Shehu ke ta kokarin ganin sun samu an ba da belinsa abin ya ci tura, bisa hujjar ‘yan sanda cewa ba su gama bincikensu ba.

A jiya Juma’a bayan kammala binciken jiya, babban Sufeto-janar na ‘yan sanda ya ba da umurnin a ci gaba da tsare shi zuwa ranar Litinin.

A jiya an kai Mahadi Shehu wajen tsare wadanda ake zargi a sashen binciken na Hukumar ‘yan sandan kasa da ke Abuja, wanda a can ya kwana zuwa yau.

Mun kira lambobin Mahadi Shehu da muke da su don yi wa labarinmu adalci, amma tana shiga ba a dauka.

Mun aika masa da sakon rubutu ta waya, shi ma har zuwa rubuta labarin nan ba amsa.

Amma daya daga cikin Lauyoyinsa ya tabbatar mana suna kokarin ganin cewa zuwa ranar Litinin sun samu ko dai a ba shi beli ko a kai shi kotu su nemi belinsa a can, kamar yadda ‘yancinsa wanda tsarin mulki ya ba shi a matsayinsa na dan kasa.

Matsalar Mahadi da Hukumar ‘yan sanda ta kasa ta fara ne da wata wasika wadda gwamnatin Katsina ta rubutu wa babban Sufeto-janar na ‘yan sanda a ranar 15/10/2020.

Takardar wadda babban Editan jaridar nan ya gani ido da ido tana da taken korafi a kan wannan mai suna Mahadi Shehu wanda ya mallaki wasu takardun karya na gwamnatin Jiha Katsina, yana kuma tunzura al’ummar Katsina su kyamaci gwamnatin.

Takardar ta korafin gwamnatin Katsina, babban Sufeto-janar na ‘yan sanda ya sanya mata hannu a ranar 18/11/2020. Ya tura ta ga daya daga cikin jami’anta da umurnin a bincika a kawo masa bayani, kamar yadda muka gani an rubuta a takardar.

Tun lokacin rundunar ‘yan sanda ta kasa suka fara neman hanyar da za su bi su kawo Mahadi Shehu don fara binciken, sai a ranar Larabar da ta gabata 25/11/2020 Mahadi Shehu ya kai kansa Hukumar ‘yan sanda ta kasa, wanda suka fara bincike, suke kuma tsare da shi.

A lokacin da yake bidiyonsa na fallasa, ya saki bidiyo har 101, ya yi wasu da ba a kai ga sakinsu ba. Kila a sake su koda yana a wajen yan sanda a tsare

Ya dora takardu guda 219, wadanda duk jaridun sun sauke su, suna nazarinsu. ya saki hotuna 301.
________________________________________________
Jaridar Taskar Labarai jarida ce mai zaman kanta da aka kafa don binciken musamman da kawo maku labarai da dumi-duminsu, tana a bisa shafin yanar gizo na www.taskarlabarai.com tun shekarar 2017. Tana kuma bisa shafukan sada zumunta na Facebook, da taken jaridar taskar labarai. WhatsApp da sauran shafukan sada zumunta. Tana da yar’uwa ta Turanci mai suna The Links News da ke a www.thelinksnews.com da kanwa mai suna Katsina City News da ke www.katsinacitynews.com. Duk suna bisa shafukan sada zumunta. Duk sako a aiko ga 07043777779.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here