AC Milan ta dare a saman Teburin Serie A

0
148

AC Milan ta dare a saman Teburin Serie A

Daga Ibrahim Ham is u

Kungiyar kwallon kafa ta AC Milan ta cigaba da kasancewa a saman teburin a gasar Serie a bayan ta lallasa Fiorentina 2-0

Romagnoli da Kessie sun taimakawa Ac Milan da kwallaye biyu yayin da ta lallasa Fiorentina 2-0 kuma ta cigaba da kasancewa a saman teburin gasar Serie A da maki 23, yayin da ita ma kungiyar Bologna ta lallasa Crotone 1-0 duk dai a gasar ta Serie A.

Ta bangaren gasar Ligue 1 kuwa kungiyar Angers ta lallasa Lens 1-0 yayin da Lorient tasha kashi 1-0 a hannun Montpellier sai Stade Brestois tayi nasarar cin Mets 2-0, ita kuma Monaco taci Nimes 3-0.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here