An karrama Fauziyya D. Sulaiman
Kano Correspondents Chapel ta karrama fitatciyar marubuciya, kuma mai aikin tallafawa jama’a, Fauziyya D. Sulaiman.
An bata lambar yabo ne a kan ayyukan da take na jin ƙan al’umma.
Amon Nasara na taya ta murna a bisa wannan nasara, da fatan wannan zai ƙara mata ƙaimi na aikin alheri da take yi. Allah ya yi jagora.