Jamian tsaro sun kama Abdulrashid Maina a Kasar Nijar

0

Jamian tsaro sun kama Abdulrashid Maina a Kasar Nijar

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na cewa an kama tsohon shugaban hukumar gyaran Fansho ta kasa, Abdulrashid Maina.

Jami’an tsaron kasar ne dake aiki na musamman suka kamashi da hadin gwiwar EFCC. An yi kamenne da yammacin Ranar Litinin.

PRNigeria ta bayyana cewa EFCC ta samu labarin tserewar Maina kasar Nijar inda ta yi gaggawar sanar da hukumomin kasar.

Ana dai zargin Maina ne da almundahanar naira Biliyan Biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here