PDP ta ja hankalin matasanta kan su fito ranar zabe
Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau
Shugaban Jam’iayr PDP a jihar zamfara ,Hon Tukur Umar Danfulani ya ja hankalin matasan jam’iyar da su fito kwasu da kwarkwatansu a ranar zabe don kwalliya ta biya kudin sabulu.
Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa wurin bikin kaddamar da yakin Neman zabe da jam’iyar ta gudanar a garin Bakura .
Ya kara da cewa wannan gwamnati ,gwamnati ce ta matasa kama daga gwamnan jihar zamfara, Hon Bello Muhammad matawalle da mataimakinsa ,Hon Mahadi Aliyu Gusau da shugaban majalisar Dokoki ta jiha, Hon Nasiru Mu’azu magarya duk matasa ne .
Don haka yace matasa su basu amana ba zasuci amanarsu ba, don haka matasa su zabi matashi Dan uwansu, shine Hon Ibrahim T. Tukur a matsayin Dan majalisa mai wakiltar Bakura, a wannan jam’iyar tasu ta PDP.
A nasa jawabin a wurin taron ya bayyana cewa mutane suyi hakuri saboda gwamna bazai sami zuwa ba shine ya wakilce shi , don haka ya ruki Nagoya bayansu su kasance tsintsiya madaurinki daya, su fito su bada goyon baya ranar zabe.
Ya kuma bukaci magoya bayansu su zama masu bin doka da oda, kamar yadda aka San ‘ya’yan jam’iyar PDP, wajan nuna kyawawan dabi’u.
A nasa jawabin Dan takaran jam’iyar PDP ,Hon Ibrahim T. Tukur ya baiwa jama’ar wannan jam’iyar tabbacin wakilci me ma’ana kuma mai inganci , wanda ba za’ayi danasani ba matukar aka zabeshi.
Dubban magoya bayan jam’iyar ne suka halarci taron , musammam sanatoci da ‘yan majilisar taraiya dana jiha, sai dai abin da ya baiwa jama’a mamaki shine yadda matasa suka shiga ihun bamaso bamaso a lokacin da shugaban yakin Neman zaben, kuma Dan majalisar taraiya mai wakiltar Anka, Hon Lawali Hanssan Anka yake jawabi.