YADDA NA SAYAR WA MAHADI TAKARDUN KARYA

0

YADDA NA SAYAR WA MAHADI TAKARDUN KARYA…

@ jaridar taskar labarai

Alhaji Mahadi Shehu ya yi suna a kwarmata zarge-zargen sata da cin kudin gwamnatin Katsina a yanar gizo da sauran kafafen yada labarai. A sakon sa yakan kafa hujja da hoto ko takardun da ya samu.

Takardun da ke wajensa ba shi yake kirkirar su ba, kawo masa ake, wasu yakan siya ne ya biya da kudi masu yawa.

Duk wata takarda da ya saki a yanar gizo mu a Taskar Labarai mun sauke ta, wasu muna nazarin su.

Daga cikin abin da muka rika bin diddigi shi ne gano su wa ke sayar wa Mahadi takardun da yake amfani da su? Takardun gaskiya ne? Ko na karya ne da aka kirkira. Wannan aikin muna a kai har yanzu.

An kama mutane da dama, wasu na gidan yari, wasu ana binciken su, wasu an kai su kotu a kan zargin suna cikin gwamnati suna kuma ba Mahadi Shehu takardu.

Mun hadu da wani matashi da ya amince ya fada mana daki-daki kuma dalla-dallar yadda ya hadu da Mahdi Shehu da kuma yadda ya kirkiri wasu takardu ya sai da masa a matsayin na gaskiya ingantattu.

Duk yankin Daura da duniyar yanar gizo a Jihar Katsina da cikin kungiyoyin matasa sunan Lawal Adamu Shunku ba boyayye bane.

Mun hadu da shi domin hirar nan. Adamu matashi ne mai kwarjini, kuma ba shi da tsoro, wanda daga ganin sa ka san ya san abin da yake.

Mun dauki muryarsa baki daya. Daga cikinta muka zakulo maku wannan labarin.

FADA MANA SUNANKA DA INDA KAKE AIKI?
Sunana Lawal Adamu Shunku. Ina da mata da ‘ya’ya. Ina aiki ne da Hukumar Ilmi ta Jihar Katsina, inda na rike wasu ofis-ofis a hedikwatar Hukumar kafin a yi mani taransfa a matsayin Malamin makaranta a garin Mai Adua, wanda nake zargin an yi mani haka ne saboda bambancin ra’ayin siyasa da kuma matsayin da nakan dauka, a kan komai ba na jin shakkar in fadi ra’ayina.

WACE IRIN GUDUMMAWA KA BA APC?
Da ni aka yi wa APC wahala a 2015. Ni da su Saifullahi Mato Kankara muka rika tona asirin gwamnatin PDP ta lokacin.

A shekarar 2019 duk yakin neman zaben da aka yi da ni aka yi. Rubuce-rubucena sun yi tasiri sosai a kamfen a yanar gizo, musamman yankin Daura.

Ban san me na yi ba, kuma har yanzu ba a fada mani laifina ba a Hukumar Ilmi ta Jihar Katsina ba, ina aiki da rike da wani ofis aka rage mani daraja zuwa Malamin makaranta mai koyarwa a ji, aka kuma kai ni garin Mai Adua”.

YA KA SAN MAHADI?
A Facebook na ga ya fara BIDIYO. Ni ne daga duk yankin Daura na fara ba shi amsa, ina mai da masa martani, ba wanda ya sa ni, amma ina kishin Jihata ne da jam’iyyata da kuma gwamnatin da nake jin da ni aka kafa ta”

YA KUKA FARA MAGANA DA MAHADI?
Wani mutum mai suna Mustafa Radda shi ne ya yi mani waya cewa shi yana tare da Mahadi, kuma yana son magana da ni a matsayin dan APC da ya yi wahala aka watsar da shi, kuma an ji na rike wani ofis a Hukumar Ilmi, wanda ba zan rasa wasu takardun sirri ba a wajena, don Mahadi shirye yake ya sayi wadannan takardun.

Da na ji haka na fada wa wani aminina na siyasa duk yadda aka yi, na kuma fada wa wani Lauya, na kuma shaida wa Ubangidana a siyasa.

Mustafa Radda ya ci gaba da yi mani waya A kan in ba da hadin kai. Wata rana sai kawai ya bugo mani ya hada ni da MAHADI. Mun dade a waya yana fadi mani in zo Kaduna mu zauna duk abin da nake so za a yi mani.

Wata rana na shirya muka nufi Kaduna, ni, Lauyana, Mustafa Radda, sai wani yaron Mahadi da ke nan Katsina wanda ake kira da ATK.

Mun fara zama da Mahadi a gidansa, Lauyana ya fada masa cewa duk muna da abin da yake so, amma sai an tattauna me zai bayar kafin a ba shi.

Na yi masa bayanin duk inda na zauna da takardun da nake ikirarin ina da su. Mahadi ya gamsu. Daga gidansa ya ce mu je ofis. A can din ne ya nuna mani wasu takardun da yake da su, ya kuma nuna mana kudi Daloli. Ya ce kudi ba matsalarsa ba ce.

Ya ce gwagwarmaya ce, an fara, kuma sai an kai karshe. Ya ce ya ba mu kwanaki mu yi shawara mu dawo masa. A ranar dubu 20 kacal ya ba mu mu sha mai.

Daga nan sai yaron Mahdi mai suna ATK da ya dame ni da waya, in zo a yi harkar arziki in samu shi ma ya ci wani abu, a rana sai ya bugo mani waya sau 30.

Shi ma Mahadi ya rika damuna da waya har yanzu ban yi shawara ba? Mahadi waya, ATK waya, haka kullum nake fama.

WAYE ATK?
ATK wani yaron Mahadi ne a a Katsina. Duk wanda Mahadi ke son magana da shi, shi ake turawa, duk sakon Mahadi shi ne ke shiga tsakani, duk abin da ake son ya isa wajen Mahadi ta hannunsa ake bi.

KUN SAKE HADUWA DA MAHADI
Wata rana ATK ya bugo mani waya, ya roke ni in zo Kano Mahadi zai zo mu hadu. Ya ce in zo a yi harkar arziki shi ma ya samu.

Mahadi ma ya kira ni ya roke ni mu hadu a Kano, amma in zo da wasu takardun da ke hannuna ko kadan ne. Na amince zan zo a ranar. Na shirya wasu takardu guda shida na bogi. Na yi masu duk yadda za a ga kamar na gaskiya ne. Na shirya wadannan takardun saboda dalilai daban-daban da kuma matsin da ATK da Mahadi ke mani in kawo masu wasu takardun.

Da safiyar ranar da muka yi za mu hadu da Mahadi karfe 1:00 ta yi mani a Kano. Muka hadu da ATK a wani otel yana tare da dansa. Daga nan sai ga Mahadi su biyu yana tare da wani Manajansa.

Mun tattauna da Mahadi ta tsawon lokaci, na dauki takardun nan na mika masa, ya duba, sannan nan ya ce me za a ba ni? Na ce na kawo masa ne a matsayin gudummuwa ta a gwagwarmayar da yake yi. Ya ji dadi ya ce lallai ni abokin tafiya ne.

Ya ce zai saki wata takarda, in ya sake ta zai so in jagoranci shirya zanga-zangar matasa ta nuna fushin yadda ake sata a Katsina kowa ya yi shiru. Ya ce ko nawa ne zai dauki nauyi.

Ya kuma ce zai kafa wani gidan talabijin mai suna Dialogue TV, yana son in ya fara mu yayata da tallata ta. Ya ce zai yi wani tsari na samun ‘Data’ ta shiga yanar gizo kyauta ga duk yake tare da talabijin din.

Bayan mun gama, ya ce zai ba ATK sako ya kawo min. ATK ya kawo mani dubu 200, a cikin na dauki dubu 20 na ba dansa, amma daga baya Mahadi ya shaida mani cewa dubu 500 ya ba ATK ya ba ni.

Sai dai tun daga ranar ATK bai sake nema na ba, ban kuma neme shi ba.

GWAMNATI TA BINCIKE KA?
Wata rana ina zaune aka kira ni a ofishin Kwamishinan Boget, Alhaji Farouk Jobe, aka ce in zo. Ina zuwa na ga kwamiti ne na mutane shida aka kira ni gabansu. Aka fito mani da takardun da na ba Mahadi Shehu aka ce na san wadannan? Na ce kwarai kuwa. Nan ne na ba su labarin duk yadda aka yi.

Kwamitin sun saurare ni, sun saurari hujjojin da na ba su, suka kuma gamsu, suka ce in tafi.

WA KAKE ZARGI?
Ban zargin kowa sai mutum daya, amma na bar wa kaina, domin takardun nan na karya ni kadai na shirya su. Mahadi kawai na ba hannu da hannu, sai ATK da dansa da Manajan Mahadi da ke gefe suna kallo.

Daga baya na samu labarin wasu jami’an gwamnati sun dasa masu ba su labari a kewaye da Mahadi, duk wanda ya gana da shi suna samun labari, duk wanda ya kai takardu ana sani.

WANE MATAKI KA DAUKA DA FARA HUDDA DA MAHADI?
Babban matakin da na dauka shi ne duk wata waya ko ganawa ina fada wa wani ubangidana a siyasa. Wani lokacin ma don in tabbatar masa a gabansa nake magana da Mahadi ko ATK, in kuma bude muryar waya ta kowa na ji. Ina kuma ba da shawarar ga abin da ya kamata su yi..

Na fada wa kwamitin wannan ubangidan nawa ko waye, na kuma ce su je su bincike shi ko su kira shi ga ni ga shi in ba mu yi haka ba.

Wannan yana daya daga cikin hujjojin da kwamitin ya sa suka tausaya mani, suka kuma gamsu da ni.

KO A HAKA MAHADI KE SAMUN TAKARDUNSA?
A irin haka ne. Saboda yana biyan kudi, wani lokaci sai a hada masa takardu na karya a ba shi don a amshi kudinsa.

Akwai takardun da Mahadi ya nuna mani, ina ganin su na gane na karya ne, irin wadanda na ba shi ne.
_______________________________________________
Taskar Labarai na a bisa shafin yanar gizo na www.taskarlabarai.com da sauran shafukan sada zumunta. Katsina City News na a bisa shafin yanar gizo na www.katsinacitynews.com da Facebook group .Facebook page, YouTube da sauran shafukan sada zumunta.
The Links News na a bisa shafin yanar gizo na www.thelinksnews.com da sauran shafukan sada zumunta. Sako kira a aiko ga 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here