Zamfara ta kaddamar da kwamitin yaki da cin zarafin mata da kananan yara a fadin jihar
Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau
Gwamnan Jihar Zamfara Hon. Bello Mohammed a yau ya kaddamar da kwamitin yaki da cin zarafin mata da kananan yara ,yana mai sake jaddada kudirin gwamnatin sa na baiwa mata kulawa .
Matawalle ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa wurin kaddamar da kwamitin a gidan gwamnati a gusau,Ya ce a matsayin wannan gwamnati mai rikon amana da kare rayukan jama’arta da inganta jin dadinsu.
Ya kara da cewa za ta dauki matakai na kawo karshen cin zarafin mata da kananan yara wadanda ya ce suna wahala matuka musamman a matsugunansu tare da shiga mawuyacin hali sakamakon ayyukan yan bindiga a wasu yankuna na jihar.
Matawalle ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da hada kai da kungiyoyi masu zaman kansu don bunkasa hadin gwiwar da ake bukata don cimma burin da ake bukata na wayar da kan mata da yara kanana da kuma hanyoyin magance matsalolin.
Ya ce musamman ganin cewa Musulunci ya ba mata muhimmiyar kulawa tare da kula da zamantakewar da gwamnati za ta ginu a kansu, musamman ta hanyar amfani da kyawawan halaye na mace.
Gwamnan ya kara da cewa gwamnatinsa tana aiwatar da wani shiri na karfafa mata wanda Uwargidan Shugaban kasar ta yi, da sake fasalin Ma’aikatar harkokin Mata don sanya yara , kuma za ta ci gaba da kyawawan manufofin da za su inganta rayuwar al’umma.
Matawalle ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da jajircewa don hana cin zarafin mata da kuma ci gaba da kokarin da ake yi a yanzu don gano hanyoyin magance wadannan munanan laifuka na cin zarafin bil’adama tare da aiwatar da dukkan dokokin da suka shafi mata da yara.
A cewarsa, tuni Majalisar Dokokin Jihar ta fara aiki kan yadda za a sanya dokar kare hakkin yara wacce ya yi alkawarin tabbatar da ita da zaran majalisar ta zartar da shi.