An dakatar da Dagatai biyu da suka kwashe Tallafin Kurona a Kano

0

An dakatar da Dagatai biyu da suka kwashe Tallafin Kurona a Kano

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Masarautar Rano da ke jihar Kano ta dakatar da Dagatai guda biyu ake zarginsu da ɓoye kayan tallafin kurona da gwamnati ta bayar a rabawa talakawa.

Chiroman Rano kuma hakimin Rano Alhaji Manniru Tafida Abubakar ILa ne ya dakatar da dagatan guda biyu, bisa umarnin mai martaba Sarkin Rano Alhaji Muhammadu Kabiru Inuwa.

Wadanda aka dakatar sun haɗa da Umar Yusuf, wanda shi ne dagacin Zurgu da kuma Kamilu Zambur da shi kuma ya ke a matsayin Dagacin Zambur, ana zarginsu da ƙin rabawa talakawansu kayayyakin abinci wanda gwamnati ta bayar domin ragewa al’umma radadin rayuwa.

Tuni dai aka aike da wakilci zuwa ƙasar dagatan da abin ya shafa.

Idan baa manta ba dai makwanni biyu da su ka gabata ma dai aka samu rahoton kwamandan Hisbah na karamar hukumar Dala Siyudi Muhammad Hassan, da zargin wawure tallafin kurona da karamar Hukumar Dala ta baiwa jami’an Hisbar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here