FARASHIN BUHUN SHINKAFA ZAI DAWO N19,000 A NIGERIYA__ RIPAN
Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Kungiyar masu sarrafa shinkafa ta Nigeria, “Rice Processors Association of Nigeria”, RIPAN, ta ce sun amince da karya farashin shinkafa zuwa Naira Dubu Goma Sha Tara, (50kg a N19,000) farashin babban buhu,
Kungiyar ta ce sabon farashin dai zai fara aiki ne daga ranar 14 ga watan Disamba da muke ciki.
Babban jami’in kungiyar RIPAN kuma Shugaban kwamitin kar ta kwana na da gwamnatin tarayya ta kafa a kan farashin shinkafa Aminu Ahmed ne ya shaidawa jaridar Daily Nigerian cewa, hakan na zuwa ne bayan ganawarsu da Babban Bankin Nigeriya CBN, a wani mataki na rage radadin talauci da tsadar kayan abinci a Nigeriya.
A halin da ake ciki yanzu farashin buhun Shinkafa a Nigeriya yana kai kaiwa daga N28,000, zuwa N35,000 ko ma fiye da haka.