Majalisar Dattawa ta amince da naɗin Yakubu a matsayin Shugaban INEC

0

Majalisar Dattawa ta amince da naɗin Yakubu a matsayin Shugaban INEC

A ranar Talata Majalisar Dattawa ta amince da naɗin Farfesa Mahmood Yakubu a matsayin Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) a karo na biyu.

Wannan tabbacin da majalisar ta yi masa ya biyo bayan miƙa rahoton da shugaban Kwamitin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa na majalisar, Sanata Kabiru Gaya, ya yi a lokacin zaman majalisar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa tun a ranar 25 ga Nuwamba ne Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa da sunan Yakubu a matsayin zaɓin sa na Shugaban INEC a karo na biyu bayan wa’adin sa na farko ya ƙare.

Lokacin da ya ke miƙa rahoton, Sanata Gaya ya ce a lokacin da ‘yan kwamitin su ke aikin tantance wanda aka zaɓan, sun gano cewa mutum ne wanda zai iya aikin kuma ya dace da wannan sabon naɗin nasa.

Ya ce: “Kwamitin ya gano cewa babu wata takardar tuhuma ko rashin amincewa da shi da aka rubuto, kuma ya nuna zurfin sani, sannan mutum ne mai nagartar halayya.”

Ya ƙara da cewa tabbatar da sake naɗin an yi shi ne a ƙarƙashin Sashe na 153(1F) na kundin Tsarin Mulki.

Yayin da yake sa baki a tattaunawa kan al’amarin, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan, Omo Ovie-Agege, ya ce, “Wannan shi ne karo na farko da aka sake zaɓen Shugaban INEC ya yi wa’adi na biyu a muƙamin sa.

“Ya kamata a yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari domin ya hango abin da yawancin ‘yan Nijeriya su ka gani wajen yadda Farfesa Yakubu ya riƙa gudanar da al’amuran INEC a tsawon shekaru biyar da su ka gabata.”

Ya ce su ma ‘yan kwamitin da su ka bada shawarar a tabbatar wa da Yakubu da wannan naɗi na wa’adi na biyu, sun nuna akwai ƙa’idojin da aka rataya a wuyan INEC a dokar da ta kafa ta, wato Dokar Zaɓe.

See also  THE BUHARI ADMINISTRATION IS SET TO CLEAR ALL PENSION BENEFITS OF NITEL AND M-TEL WORKERS!

Ya ce, “Saboda haka, sun kawo muhimman dabaru kan yadda za mu iya kawo gyara a tsarin ta hanyar amincewa da wanda aka zaɓa ɗin.”

Shi ma Sanata James Manager (PDP-Delta), ya bayyana wanda aka zaɓa ɗin da cewar mutum ne wanda ya nuna tsantsar bajinta da adalci a wajen gudanar da zaɓuɓɓuka a zamanin wa’adin sa na farko.

Ya ce: “Ina kira ga wanda aka zaɓa ɗin da ya ƙara yin kaffa-kaffa da ma’aikatan INEC. Dalili shi ne sunan da zai yi bayan an ƙara naɗa shi ya fi nasarorin da ya samu a baya.

“Ya kamata ya yi aikin domin ya bar baya da kyau, wanda zai fi abin da ya yi a baya muhimmanci.”

Sanata Sandy Onor (PDP-Cross River) kuma ya ce Farfesa Yakubu alƙali ne wanda bai nuna wariya, ya ƙara da cewa naɗin da aka yi masa ya dace da shi ƙwarai da gaske.

Ya ce: “Wanda aka zaɓan ya nuna ƙwarewa, kuma ba shakka ya nuna cewa shi alƙali ne wanda ba ya nuna wariya. A yau, ‘yan siyasa ba su shiga zaɓe da fargabar ko za a musguna masu.

“Idan mu ka dubi nasarorin sa a wa’adin sa na farko, za mu ga cewar zai ma yi aiki fiye da da a wannan wa’adin na biyu.

“Ina sa ran in ga idan zai maida dukkan al’amurran zaɓen mu su koma ta intanet da komfuta kawai fiye da yadda ya yi.”

Ban da Yakubu, a yau ɗin ma Majalisar Dattawan ta amince da naɗin Sanusi Garba a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC). Haka kuma ta amince da naɗin
Dakta Musiliu Olalekan Oseni a matsayin Mataimakin Shugaban hukumar da kuma Aisha Mahmud a matsayin Kwamishina a hukumar ta NERC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here