Tsohon mataimakin gwamna ya sauya sheka daga APC zuwa PDP a jihar Zamfara

0

Tsohon mataimakin gwamna ya sauya sheka daga APC zuwa PDP a jihar Zamfara

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Tsohon mataimakin gwamna a jihar Zamfara , Ibrahim Wakkala muhammad ya fice daga jam’iyyar APC (All Progressive Congress)zuwa jam’iyyar PDP (Peoples Democratic Party)

Ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya kira a gidansa da ke Gusau, babban birnin jihar, Hon Ibrahim wakkala wanda ya yi zama a matsayin mataimakin gwamna na tsawon shekara takwas,ya ce ya yanke shawarar ne bayan ya tuntubi magoya bayansa da masu bashi shawara da dama.

Ya ce “Bayan na tuntubi tsohon gwamna na, Abdulaziz Yari, da iyalina, da abokai na, da masu yi min fatan alheri da kuma masu ba da shawara kan harkokin siyasa, tare da gudanar da addu’oi don neman Allah ya tabbatar mani da abinda yafi zama alhairi, don haka daga yau na riga na koma PDP,” in ji Wakkala.

Ya kara da cewa an jima ana ta yada jita-jita, Wanda ta zagaye ko’ina na tsawon shekaru biyu cewa ya sauya sheka zuwa PDP sakamakon kusancinsa da gwamna Bello Mohammed matawalle.

Tsohon mataimakin gwamnan ya ce “Duk tsawon lokacin, gwamna Bello Muhammad yana ta saurara mani, kuma yana karbar shawarwarina kan ci gaban jihar da kuma tsaronta, wanda nake ganin hakan a matsayin girmamawa gare ni” in ji shi.

“Gwamna Bello matalle ya roke ni da na shiga jam’iyyarsa,Bayan tuntubar abokaina na siyasa, yanzu na koma PDP a mazabata ta Galadima, dake karamar hukuma ta , da kuma jiha, ”inji shi.

Wakkala ya ci gaba da cewa zai ci gaba da kasancewa mai sada zumunci ga dukkan abokai na siyasa da abokan hulda ba tare da la’akari da sauya shekarsa ba zuwa sabuwar jam’iyyarsa ba ta PDP.

Wakkala ya ce”Kafin yanke shawara na barin APC zuwa PDP, ya rubuta wa tsohon maigidansa, Abdulaziz Yari Abubakar da tsohuwar jam’iyyarsa ta APC a jihar,” ya kuma bukaci al’ummar jihar dasu hada karfi da karfe don kawo karshen wannan matsala ta tsaro don ba matsala bace da za’a sanya siyasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here