YAN SANDA SUNYI BORE A BATSARI TA JAHAR KATSINA
….. soja sun so taka masu burki
…………sarkin Ruma ya shiga tsakani
Daga misbahu Batsari
@ jaridar taskar labarai
A yau alhamis 3 /12/2020 dai lokacin da al’umma ke hada hada domin cin kasuwar Batsari.
kwatsam sai jami an ‘yan sanda suka sanya shinge a duk hanyoyin shigowa kasuwar inda suka datse babban titin shigowa gari zuwa kasuwa daidai asibiti.
yan kasuwa da sauran jamaa duk sun rude ganin yadda lamarin ke neman kazancewa domin sun hana shiga sun hana fita.
Ana cikin haka sai jamian Soja suka zo suka cire shinge da yan sanda suka kafa a daidai babbar asibitin Batsari.
Su kuma jamian’yan sanda suka sake maida shingen, wannan ya sanya musayar zafafan kalamai tsakanin su. Yan sanda da sojojin
Wata majiya ta nuna cewa yan sandan suna kokarin hana cin kasuwar ne, domin nuna fishin su kan kin biyan wasu kudaden su na alawus da gwamnatin jaha tayi na wata daya kacal
sarkin Rumah Katsina hakimin Batsari, Alhaji Tukur Muazu Rumah ya halarci wajen har ma ya sasanta yan sandan da sojojin . Yan sanda na son hana mutane cin kasuwa soja na son a kyale mutane su shiga kasuwa.
Bayan shiga tsakanin da sarkin Ruma yayi lamurra su cigaba kamar yadda aka saba.munyi kokarin jin ta bakin kakakin rundunar yan sanda ya jaha wayar bata shiga.