HOTUNAN MAHADI SHEHU A WAJEN YAN SANDA

0

HOTUNAN MAHADI SHEHU A WAJEN YAN SANDA
Muhammad Ahmad
@ Jaridar taskar labarai
Wasu hotuna sun bayyana na Alhaji mahadi shehu shugaban rukunin kamfanonin dialogue. Wanda yanzu haka yake wajen yan sanda suna binciken sa akan wata takarda koke da gwamnatin jahar katsina ta shigar a kansa a ranar 15 ga watan oktoba na 2020.
Takardar tana neman hukumar yan sanda su bincika akan mahadi na amfani da wasu takardun karya don tunzura mutanen katsina.
Hotunan sun nuna Alhaji mahadi shehu yana bisa kujerar daukar marasa lafiya , hotunan Wadanda jaridun taskar labarai suka tabbatar da shine, sun kuma nuna wani mutum yana Mika masa wasu takardu.
Taskar labarai ta gano cewa takardun da ake bashi na wata kara ce da aka shigar da mahadi shehu a wata kotu a katsina, takardun sammacin ne da aka kasa bashi sai yanzu aka kai masa su a inda yake a tsare .
Wata majiya tace duk kararrakin da aka kai mahadi shehu sai yanzu ake samun damar kai masa sammacin , don a baya an rasa ina za same shi a kai masa.
Iyalan mahadi sun koka ga jaridar Daily trust cewa rayuwar shi na cikin hatsari. A hirar da sukayi da jaridar sun tabbatar da cewa maciji ya sare shi lokacin yana tsare a wajen yan sanda.
Sunce baya da lafiya kuma yana son ganin likita.
wani jami in yan sanda ya tabbatar wa da jaridar nan cewa suna kai duk Wanda ya samu matsalar lafiya wajen su, asibitin da tayi dai dai da yanayin da yake ciki.
Wata kungiya mai rajin kare hakkin dan Adam sunyi Kira da yan sanda suyi gaggawan kammala binciken mahadi shehu su gabatar da shi a kotu kamar yadda dokar kasa ta tanada.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here