Hukumar ‘yansanda ta dakatar da taron rufe yakin Neman zaben Bakura

0

Hukumar ‘yansanda ta dakatar da taron rufe yakin Neman zaben Bakura

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Shugaban hukumar ‘yansanda mai kula da yankin sokoto ,Kebbi da zamfara, AIG Muhammad A mustafa ya bada umurnin dakatar da taron rufe yakin Neman zaben Bakura.

AIG mustafa yayi wannan bayanin ne a garin Bakura a lokacin da yake yiwa manema labarai bayani, ya kara da cewa ganin yadda taron yazo da matsaloli wanda ya kai da rasa rayuka.

Ya kara da cewa mutun biyu sun rasa rayukansu tsakanin jiya da yau kuma wasu da dama sun sami raunka.

Sai sakamakon yadda abubuwa suka rincabe yasa gwamnantin jihar zamfara ta kafa dokar ta baci na awa ashirin da hudu, Wanda zai dauki tsawon kwana biyu, daga ranar alhamis zuwa jumu’a.

See also  MAN CITY TA YI NASARAR DAUKAKA KARA A KAN BUGA GASAR ZAKARUN TURAI

Sai dai an bayyana cewa wannan dokar ba zai hana gudanar da zaben ba a ranar asabar.

Sai dai duk da wannan umurni be hana jam’iyar APC gudanar da taronsu ba, Wanda daga bisani tsohon gwamnan jihar zamfara, Alh Abdul’aziz Yari ya rufe taron .

An gudanar da taron ne cikin tsauraron matakan tsaro, kama daga sojoji da ‘yansanda da jami’an tsaro na farin kaya da dai sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here