Kungiyar ‘Tinubu Vanguard’ ta ce sake naɗin Yakubu a INEC ya dace

0

Kungiyar ‘Tinubu Vanguard’ ta ce sake naɗin Yakubu a INEC ya dace

Wata ƙungiyar siyasa mai suna ‘Tinubu Vanguard’ ta yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari kan ƙara naɗa Farfesa Mahmoud Yakubu da ya yi a matsayin Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC).

Darakta-Janar na ƙungiyar, Dakta Johnny Ben, wanda ya yi yabon cikin wata sanarwa da ya bayar a Abuja, ya bayyana naɗin Yakubu da sunan matakin da ya dace ne.

Ya yi kira ga shugaban na INEC da ya ɗauki matakan ƙara ƙarfafa hukumar domin ya samu damar cimma nasarar shirya zaɓe nagartacce.

Ya ce: “Sake naɗa Yakubu a matsayin Shugaban INEC a wa’adi na biyu kuma na ƙarshe mataki ne da ya dace.

“Mu na yaba wa shugaban ƙasa kan wannan naɗi; haka kuma mu na yaba wa Majalisar Dattawa saboda rashin ɓata lokaci wajen tacewa da amincewa da naɗin.

“A bayyane yake cewa Yakubu ya yi aiki mai kyau a lokacin wa’adin sa na farko, ta hanyar kawo sababbin hanyoyi da su ka taimaka wa tsare-tsaren mu na gudanar da harkokin zaɓe.”

Ben ya yi kira ga gwamnati da ta gaggauta yi wa Dokar Zaɓe kwaskwarima domin a samu damar fito da tsari na gaskiya da nagarta a harkokin zaɓe kafin manyan zaɓuɓɓukan shekara ta 2023.

Ya ce, “Idan majalisa ta amince da Ƙudirin Garambawul ga Dokar Zaɓe, INEC za ta fi yin aiki da gaske kuma wanda babu makusa a tare da shi a yayin da zaɓuɓɓukan 2023 ke ƙaratowa.”

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa a ranar Talata da ta gabata ne dai Majalisar Dattawa ta amince da zaɓin Yakubu a matsayin wanda zai riƙe hukumar a karo na biyu bayan sake naɗa shi da shugaban ƙasa ya yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here