Matasa sun sanya kwamishinan kananan hukumomi da shugaban mata cikin tsaka mai wuya a zamfara

0

Matasa sun sanya kwamishinan kananan hukumomi da shugaban mata cikin tsaka mai wuya a zamfara

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Wasu yan bangan siyasa sun sanya Kwamishinan Kananan Hukumomi da ci gaban Al’umma na Jihar Zamfara, Alhaji Yahaya Chado da Shugabar Mataimakiyar Shugabar PDP ta shiyyar Zamfara ta Yamma Hajiya Ai Maradun cikin tsaka mai wuya a wurin zaben cike gurbi da ya gudana a Bakura.

Kwamishinan da ita shugaban matan sun fita da kyar daga hannun wasu da ake zargin ‘yan bangar siyasa ne a Garin Rini na Karamar Hukumar Bakura yayin kokarinsu na sanya idanu kan yadda ake gudanar da zaben fidda gwani na kujeran Danmajilisar jiha wanda ya gudana a karamar hukumar Bakura, Karamar Hukumar Bakura.

Shuwagabannin guda biyu, Wanda ‘yayan jam’iyar PDP ne a jihar wadanda suka ziyarci mazabar Shiyyar Galadima 008 a garin Rini yayin gudanar da zaben.

‘yan daban wadanda ake zargin‘ yan jam’iyyar APC ne sun bukacesu dasu fice daga rumfar zaben amma tare da sa hannun tsohon kwamishinan kananan hukumomi da lamuran masarautu. , Alhaji Muttaka Rini da kuma jami’an ‘yan sanda wadanda suka kwantar da rikicin ta hanyar harbe harben bindiga a sama ,kuma suka tafi da su.

See also  Shugaban masu buƙata na ƙasa yace tabbas Sen, Atiku Bagudu jagorane kuma abun koyi.

Su dai wadannan mutane biyu sai da aka sanya su cikin mota suka kuma kwashe sama da minti 25 a cikin motarsu , har zuwa lokacin da wannan tagagin ya kwanta, sai da ’yan sanda suka shiga tsakani suka cece su .

A wani mai kama da wannan cikin wata hira da wakilinmu yayi da wani mai jefa kuri’a Malam Salman Muhammad Rini ya koka kan yadda wasu ‘yan bangar siyasa dauke da nau’ikan makamai masu hadari suka samesu a yayin da suke kokarin amfani da katinsu na zabe a rumfarsu ta Oroji da ke Garin Rini a lokacin zaben.

wasu da suke zargin ‘yanbindiga ne sun yi kokarin koransu, har sukayi masu barazanar harbi, sai dai basu sami nasara ba, duk da suna dauke da bindigogi kirar AK 47, sai dai duk da wannan barazana be sanya jama’a suka watse ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here