Ma’aikatan zabe sun Bace : ,zabe be kammalu ba a zamfara

0

Ma’aikatan zabe sun Bace : ,zabe be kammalu ba a zamfara

Daga Shuaibu Ibrahim Gusau

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana zaben maye gurbin mazabar Bakura a jihar Zamfara, wanda aka gudanar a ranar Asabar bai kammalu ba sakamakon tashe tashen hankula a wasu gurare.

Jami’in tattara sakamakon zaben, Farfesa Ibrahim Magawata wanda ya yi magana da manema labarai a safiyar ranar Lahadi ,ya ce an soke sakamakon zaben na wasu rumfunan zabe a yankin Bakura.

Da yake karin haske kan guraren da aka soke zabukan ,a cewar sa Farfesa Magawata, yace runfunan zaben da aka soke suna da jimillar kuri’u Dubu goma sha daya da dari hudu da Ashirin da tara 11,429.

Amma ya bayyana cewa ya zuwa yanzu dan takarar PDP, Alhaji Ibrahim Tudu ya samu kuri’u 18645, yayin da dan takarar APC, Alhaji Bello Dankande Gamji ya samu 16464.

Sai dai saka makon tashe tashen hakkula da amfani da ‘yan bindiga da ake zargin wasu sunyi ya janyo bacewar wasu mutane ma’aikatan zabe na wucin gadi, Wanda har yanzu ba’a san inda ma,aikatan suke ba.

Ya zuwa yanzu dai ba’a sanya ranar da za a kammala zaben cike gurbin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here