Bazamu shiga zabe ba matukar ba’a bamu tabbacin tsare rayukanmu ba…..Yari
Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau
Tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar ya zargi gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin gwamna Bello Mohammed Matawalle ta hanyar hada kai da wasu jami’an tsaro don yin magudi a zaben cike gurbi a karamar hukumar Bakura, da ba a kammala ba kamar yadda hukumar zabe (INEC) ta bayyana ta hanyar zagi da cin zarafin ‘ya’yan jam’iyyar APC (All Progressive Congress. )
Yari ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan matsayarsu kan sakamakon zaben a gidansa da ke karamar Hukumar Talata Mafara .
Ya kara da cewa ba za su shiga zaben fidda gwani mai zuwa ba idan har jami’an tsaro musamman ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro suka kasa sasanta batun kare rayuka da dukiyoyin mambobin APC da kuma zaben su yayin gudanar da zaben cike gurbin da ke zuwa nan gaba .
Ya ci gaba da cewa “Mun lura cewa wasu daga cikin jami’an tsaron da aka tura don tabbatar da gudanar da zaben cikin lumana gwamnatin jihar ta shawo kansu tare da ba da damar yin magudi da sayen kuri’u tare da karfafa wa wasu ‘yan PDP hayar ‘yan bangar siyasa, suka kuma kai wa mambobinmu hari tare da rusa tsarin da ake gudanar da zaben.
Tsohon gwamnan ya ce amma ba za mu shiga zaben ba idan har ba a tabbatar da tsaronmu da na wadanda suke zabe a yayin zaben maye gurbin da ba a kammala ba .