PDP ta zargi baturen hukumar zabe da nuna bangaranci a zaben Bakura
Daga Shuaibu Ibrahim Gusau
Jam’iyyar PDP mai mulki a jihar zamfara karkashin jagorancin ,Hon Bello matawalle ta zargi baturen hukumar zabe ,Wanda ya tattara sakamakon zaben cike gurbi na ranar Asabar da ta gabata a karamar hukumar Bakura da ke Jihar Zamfara, Farfesa Ibrahim Magatawa, da nuna Bangaranci.
Jami’in yakin neman zaben cike gurbi, sanata Lawalli Dan’iya ya bayyana haka a lokacin da yake yiwa manema labaru bayani a gidan gwamnati, ya kara da cewa Farfesa Ibrahim Magatawa na son bai wa Jam’iyyar APC damar da ba ta dace ba a shirin sake zaben a rumfunan zabe 14.
Ya kara da cewa bayanan da ya gabatar da yake cewa “idan APC za ta yi, za ta iya samun galaba idan har aka sake yin wani zabe a wadannan bangarorin inda aka soke zabe, cewa za su iya fin karfin PDP.
Ya ce kuma a sakamakon haka, mu sun ayyana wannan sakamakon a matsayin wanda bai kammala ba, ”ya nuna bangarancin sa.
Dan’iya ya ce “ ‘ya’yan Jam’iyyarmu sun yi mamakin lokacin da, ya bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba, ganin cewa yawan wadanda suka yi rajista a mazabu 14 ya fi 11,439 sama da bambancin 2,181 tsakanin kuri’u 18,645 da PDP ta samu da kuma kuri’u 16,464 da APC ta samu.
Magatawa ya fito fili ya ba da shawarar cewa sake zaben zai ba APC nasara a kan PDP, don haku mun bukaci a cire Farfesa Magatawa ba tare da bata lokaci ba.