AN NADA AMINU ALA DANBURAN SARKIN GOBIR

0

AN NADA AMINU ALA DANBURAN SARKIN GOBIR

Daga Ishaq Mahmood Suleiman

Ina mai amfani da wannan dama domin taya murna ga Daktan Mawaƙa, Sarkin Waƙar Ƙasar Dutse, Dujuman Ƙaraye, Ɗan Amanar Bichi, bisa wannan sabon sarauta ta da ya samu ta (ƊANBURAN SARKIN GOBIR) sarauta ce ta ƴaƴan sarakai daga asalinsa wato Masarautar Sabon Birnin Gobir ta Bawa Jangwarzo.

Haƙiƙa wannan sarauta ta ƙara fitowa tare bayyanawa duniya cewa Aminu Ala tsatso ne na sarakai, kuma daga gidan Sarauta mai daraja da ƙima, waɗanda suna daga tushen masarautun ƙasar Hausa.

Nasarori na zuwa ne a lokacin da mutum ya ke kyautata mu’amalarsa da mutane. Tabbas duk wanda Ya san Aminu Ala zai bayar da shaidarsa game da yadda yake tafiyar da rayuwarsa bisa taka-tsan-tsan kyautata wa al’umma.
Shakka babu an sanya ƙwarya a gurbinta.

Muna addu’ar Allah Ya taya shi riƙo, Ya ba shi ikon yin amfani da waɗannan ɗaukaka da Allah Ya ba shi su domin ciyar da alummarmu ta Kasar Hausa da ma kasa baki baki daya, Allah Ya tsone idon maƙiya da mahassada a cikin lamuransa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here