Buhari ya rantsar da Yakubu a matsayin Shugaban INEC a karo na biyu

0

Buhari ya rantsar da Yakubu a matsayin Shugaban INEC a karo na biyu


Shugaba Muhammadu Buhari a yau Laraba ya rantsar da Farfesa Mahmood Yakubu a matsayin Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC ), a wa’adi na biyu don gudanar da aiki na tsawon shekara biyar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewar an yi taron rantsarwar ne a jim kaɗan kafin a fara taron mako-mako na Majalisar Zartaswa ta Tarayya ta hanyar intanet a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Idan kun tuna, tun a ranar 1 ga Disamba ne Majalisar Dattawa ta amince da sake naɗin Yakubu a matsayin Shugaban na INEC.

Tabbatar da naɗin na Yakubu da majalisar ta yi ya biyo bayan rahoton da Kwamitin ta kan INEC, wanda Sanata Kabiru Gaya ke shugabanta, ya gabatar a lokacin zaman ta.

A ranar 25 ga Nuwamba ne Shugaba Buhari ya aika da sunan Yakubu ga Majalisar Dattawan domin ta amince da naɗin sa a karo na biyu.

Buhari ya sake naɗa Yakubu ne a matsayin Shugaban INEC don gudanar da aikin shekara biyar a ranar 27 ga Oktoba.

Yakubu dai shi ne mutum na farko da zai jagoranci hukumar a karo biyu.

A jawabin da ya yi ga manema labarai da ke Fadar Shugaban Ƙasa bayan an rantsar da shi, Yakubu ya sha alwashin zai ƙara zage dantse wajen tabbatar da an riƙa gudanar da zaɓuɓɓuka fisabilillahi a ƙasar nan.

Ya nanata cewa INEC za ta ci gaba da haɗa gwiwa da Majalisar Tarayya wajen tabbatar da an yi wa dokokin zaɓe garambawul a cikin lokaci.

Ya ce: “A bayyane yake cewa mun nuna a zaɓuɓɓukan da aka yi cikin ‘yan watannin nan cewa ana samun cigaba wajen shirya zaɓuɓɓuka kuma za su ci gaba da inganta kamar yadda ya kamata.

See also  Suleja-Minna road to be completed December

“Majalisar Tarayya za ta shirya taron faɗin albarkacin bakin ‘yan ƙasa a kan yi wa dokokin zaɓe garambawul.

“Wannan ya na da muhimmanci kuma a wannan karon, tare da haɗin gwiwar Majalisar Tarayya, za mu tabbatar da cewa an zartar da ƙudirin garambawul ɗin a cikin hanzari, kuma da zaran an yi hakan, zai taimaka mana ƙwarai da gaske wajen tunƙarar dukkan ƙalubalen da ke gaban mu.

“An riga an yi nisa wajen shirye-shiryen zaɓuɓɓukan shekara ta 2023; mu na buƙatar tabbaci saboda haka hurumin dokokin zaɓe na da muhimmanci, wanda idan babu shi ba za mu iya fito da namu ƙa’idojin da dokokin ba.

“Idan babu namu ƙa’idojin da dokokin, ba za mu iya kammala aiki kan kundin horas da ma’aikatan wucin-gadi da za su yi aiki a lokutan zaɓuɓɓukan ba.

“Saboda haka daga nan, zan tafi kai-tsaye zuwa Majalisar Tarayya ne, saboda a fara aiki gadan-gadan, wanda mun riga mun fara shi.’’

NAN sun fahimci cewa taron na Majalisar Zartaswa ta Tarayya da aka yi ta hanyar intanet ya samu halartar Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo, da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, da Shugaban Ma’aikatan Ofishin Shugaban Ƙasa, Farfesa Ibrahim Gambari, da Mai Bada Shawara Kan Harkokin Tsaro (NSA), Manjo-Janar Babagana Monguno (ritaya).

Sauran ‘yan majalisar da su ka halarci taron ido da ido sun haɗa da Antoni Janar kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, da Ministan Yaɗa Labarai Da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, da Ministan Ayyuka Da Gidaje, Babatunde Fashola, da Ministan Harkokin Jiragen Sama, Sanata Hadi Sirika, da Ministar Harkokin Mata, Pauline Tallen, da Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji Da Inganta Rayuwa, Sadiya Umar Farouk, da sauran su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here