Sarkin kungiyar Hausa
Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Sarkin kungiyoyin Daliban Hausa ta kasa Nura Sulaiman Janburji ya ce mafi yawan Hausawa na fitita harshen turanci ne a maimakon harshen Hausa, ya alakanta koma bayan da harshen Hausa ke samu da rashin zaburar da ‘yaya da iyaye ba sa yi, da kuma watsi da mahukunta suka yi wa harshen.
Ya ce mutane daga kasashe daban- daban na zuwa kasar nan musamman jihar Kano domin yaren Hausa,
Hanyoyin da zaa bi a dakile wannan matsalar ita ce mu dauka a ranmu cewa wayewa ita ce kai magana da harshe daya Hausa Hausa turanci turanci larabci larabci.
Hausawanmu a yanzu kwaikwa yayi ya yawa, musamman matasanmu , za ka ana kwaikoyon mawaki ko dan kwallo ko ‘yan Fim to wannan abun za mu cire a zukatanmu, idan aka cire wadannan za ka ga mun cigaba,
Ya ce duk da ya ke akwai malaman da suke gani Idan yare bai yi aro ba to ba zai cigaba ba, amma ba irin wannan aron na Ingausa ba, za ka ji bahaushe yana (Okey) da (you know)to ba irin wannan aron ake nufi ba.
Gobe ne dai kungiyar ta shirya taron Mukala da kacici-kacici mai taken ‘Idan ka cika Bahaushe’ domin Zaburarwa da habaka harshen Hausa.