Yajin aikin Malaman Jami’o’i baraza ne ga ilimi a Arewacin Kasar nan

0

Danmaje

Shugaban kungiyar wadanda suka damu da al’amuran da suka shafi arewacin Najeria, wato (Arewa Citizen Concern for Development) Alhaji Rufa’I Mukhtar Danmaje ya ce yajin aikin Malam jami’o’I na shafar al’ummar arewa ne kawai.
Danmaje na wadannan kalamai ne yayin taron manema labarai da ya gudanar a ranar Talata a nan Kano.

Ya ce la’akari da yadda arewacin kasar nan suka dogar da jami’o’in gwamnati, hakan ta sanya yankin ke shan azaba da yajin aikin.
A cewarsa kudancin kasar nan na da jami’o’I masu zaman kansu da dama, koda ana yajin aikin ba zai tabasu sosai kamar yadda ya ke taba arewa ba.

Dan maje ya kuma ce yajin aikin na malaman jami’o’i na daya daga cikin abinda ke dada ta’azzara matsalar tsaro a arewacin kasar nan.

A cewarsa matasa da dama da basu zuwa makaranta, kuma basu da aikin da za su yi hakan na jefa rayuwarsu cikin matsin da suke shiga harkar ta’addanci.

“Jami’I’o basu kyauta mana ba, kuma bamu zaci haka daga wurin manyan jami’o’in mu ba, kuma arewacin Najeriya ake cuta.

“Mune bamu da jami’o’I masu zaman kansu, mune ke da nakasu kuma mune ake dada haifar mana da wannan bala’in

“Yaran mu da suke zaune a gida dole su kirkiri abinda za su yi, wani in ya samu fitina yenta zai yi

“Yana daya daga cikin abinda ya hana mu zaman lafiya, wadannan jami’o’I da suka ce a tafi yajin aiki, ai arewacin najeriya ake cuta

Rufa’I Danmaje ya ce a kudancin kasar nan ana samun jiha daya da ke da jami’o’’I masu zaman kansu har guda bakwai, amma da wuya ka samu hakan a arewacin kasar nan.

Ya ce hanyoyin da aka bi aka nakasa arewa na da dunbin yawa, la’akari da yadda aka hana wutar lantarki, Ilimi da sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here