AN KAI WA MAKARANTAR KWANA TA KANKARA HARI.
muazu hassan
@ jaridar taskar labarai
A daren jiya da misalin karfe Goma na dare miyagun daji masu dauke da Muggan makamai suka kai Hari garin kankara ta jahar katsina. Suka kuma kai Hari a makarantar kimmiyya ta kwana dake garin inda suka shiga makarantar suka tarwatsa daliban suka tafi da wasu da har yanzu ana tantancewa.
Ganau sun shaida mana cewa, maharan sun zo a bisa babura ya kai dari uku kowa da goyo.ta wani daji da ake Kira Dan Sabau.
Maharan sun nufi makarantar kwana kai tsaye inda suka harbi wani Dan sanda da suke gadin makarantar.
Sun shiga cikin makarantar, inda maharan suka debi wasu daliban, wasu kuma suka fashe suka fantsama daji.
Binciken taskar labarai ya gano makarantar na da dalibai sama da dari takwas a dai dai lokacin da aka kai harin na jiya.
Babu daliban jss3 babu kuma na sss3 amma duk sauran daliban suna a makarantar.a jiya bayan yan taddar sun bar makarantar.an gano dalibai dari uku da hamsin da suke sake a cikin makarantar.a safiyar yau an gano wasu dari da suka gudu a daji.har yanzu ana tattarawa da tantancewa kafin a tabbatar dalibai nawa yan ta addar suka dauka.
Jami an tsaro, sun kai dauki cikin gaggawa,Wanda sama da mota talatin suna a cikin dajin da kuma garin na kankara yanzu haka.
Wakilan mu suna a garin na kankara zasu rika kawo duk abin da ya faru don haka ku Sanya ido ga shafukan jaridun taskar labarai. @ www.taskarlabarai.com da www.thelinksnews.com da kuma www.katsinacitynews.com