DALIBAN DA AKA DAUKA SUNA DAJIN ZAMFARA
Muazu Hassan
@Jaridar Taskar Labarai
Binciken da jaridar nan ta gudanar sun gano daliban makarantar kwana ta Kankara Jihar Katsina da aka sace a jiya da dare, yanzu haka suna a wani bangaren dajin cikin Jihar Zamfara.
Wasu mutanen garin da aka tattauna da su sun ce, yankin Kankara ya saba da sanin in za a kawo hari, kuma garuruwa na daukar matakin kare kansu.
Wadanda aka zanta da su sun ce, duk garin an san barayi za su zo, amma ba wanda ya yi tsammanin makarantar suka nufa.
Kauyukan da ke yankin Kankara da yawa sun yi shiri sosai na kare kansu a yankunan barayin sai suka yi ba-zata.
Da suka shiga makarantar sun kora yaran kamar shanu, sun fara ajiye su a duwatsun da ke cikin Fawwa, kamar yadda ganau suka tabbatar wa da Jaridar nan.
Fawwa, wani wuri ne da barayin nan suka mayar kamar sansaninsu. An ce sun gina ramukan karkashin kasa a wajen, sun kuma gina dakuna a wajen duwatsun.
Duwatsun Fawwa matattara ce, wadda kowa ya sanya, barayin sun yi amana da wasu kauyukan kusa da wurin ba su taba tona su, kamar yadda wani ya shaida mana.
Ganau sun tabbatar wa da Jaridar nan cewa, barayin nan da yaran nan suna kora su kamar shanu da wajen karfe 6 na safiyar yau a daidai wata koramar da ake kira Dan Sabau da ta raba Kankara ta Jihar Katsina da dajin Zamfara.
Ganau sun tabbatar wa Jaridunmu cewa wajen karfe 7 na safiyar yau Asabar, duk barayin da kuma yaran suna cikin yankin dajin Jihar Zamfara.
Ganau sun ce suna shiga yankin aka rika jin rugugin harbin bindiga na ana masu tarya ta murna da nasara irin wanda suke yi in je hari an yi nasara an dawo.