YADDA MUKA GUDO DAGA HANNUN MAHARA

0

YADDA MUKA GUDO DAGA HANNUN MAHARA .
……………. injin wani dalibin makarantar kankara
Muazu hassan
@ jaridar taskar labarai
Wani Dalibi daga daliban makarantar kwana ta kankara jahar katsina, Wanda muka sakaya sunanshi.bisa bukatar mahaifanshi,ya bayyana yadda suka gudu daga dajin da aka tsare su, bayan an sace su.
Dalibin ya bayyana cewa,bayan an tara su a cikin farfajiyar makarantar kafin a tafi dasu, wani Wanda ake ganin kamar babbansu ne yana ta waya.da ogoginsa yana kuma fada ma sauran abin da aka bashi umurni
Umurnin shine karsu su harbi dalibi karsu kashe su tabbatar ba Wanda yaji ciwo. Dalibin yace daga nan aka ce mu kama hanya.mun kwana wani wuri da ban San ko ina bane.da sassafe aka kara damu wani wajen duk a cikin daji.
Sai wannnan babban ya kara waya,sai aka rarraba mu kashi kashi.kamar yadda akan Raba mu a makaranta in zamuyi aiki.wannan babban ya rika bi yana tabbatar da komi na tafiya kamar yadda aka tsara kuma yana waya.
Daga nan wasu sai suka rika zuwa da babura suna daukar duk kason da aka basu.ni inda aka ajiye mu, Dana lura masu gadin da mai daukar mun masu yawa sai na faki idanunsu ni da wani muka gudu.
Munyi ta tafiya har muka iso bakin titi, wani mai mashin ya dauko mu.ya kawo mu wani gari daga nan muka samu wani ya kara da kawo garin kankara.
Mun tambaye shi, daliban sun kai su nawa? Dal ? Yace suna da yawan gaske.bai iya tantancewa.
Gwamnan katsina ya ba hukumar makarantar umurnin a dauko rijistar daliban baki daya a Kira uwayen daya bayan daya don tabbatar da dalibi nawa suka koma gida?in an kammala wannan sanan a tabbatar da yawan daliban har da ma da sunayen su. Da inda suka fito.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here