WADANDA SUKA JAGORANCI HARIN KANKARA

0

WADANDA SUKA JAGORANCI HARIN KANKARA

Mu’azu Hassan
@Jaridar Taskar Labarai

Binciken jaridar nan ya gano kungiyoyin masu dauke da makamai uku ne suka jagoranci harin da aka kai a makarantar dalibai ta kwana da ke garin Kankara na Jihar Katsina.

Majiya mai karfi ta tabbatar mana da cewa babban Jagoran da ya jagoranci kai harin, wani barawon daji ne mai suna Awwalun Daudawa mai shekaru 42 a duniya.

Asalinsa mutumin garin Daudawa ne na Karamar Hukumar Faskari a Jihar Katsina. Daga baya ya koma garin Dumburun na Jihar Zamfara yana yi wa Fulani kiwo.

Daga baya ya koma harkar makamai ga barayin daji. Daga bisani ya zama Gidigo shi ma.

Awwalun Daudawa ba Bafullatani ba ne, amma dadewarsa a daji ta sa yana jin Fulatanci.

Bayan ya yi karfi, sai ya shata wani yanki a bangaren Faskari na Jihar Katsina da wani bangare na Zamfara a matsayin nasa.

Awwalun Daudawa bai taba amsar maganar sulhu ba, kuma ba a taba zama da shi ba. Rayuwarsa baki daya a daji take, yana da ‘ya’ya da mata.

Majiyarmu ta ce Awwalun Daudawa ya nemi taimakon Dankarami, – wani barawon daji da ke aiki tsakanin Zamfara, Kebbi da Katsina-.

Dankarami matashi ne da yake da shekaru 33 a duniya. Ya taba karbar sulhu. Yana da mayaka masu yawan gaske a yankin.

Shi ma asalinsa ba Bafullatani ba ne. Cikakken Babarbare ne. Duk rayuwarsa a daji ya san ta.

Majiyarmu ta ce, wasu yaran Dankarami sun taimaka wa Awwalun Daudawa.

Na uku da ake jin yana cikin shi ne Idi Menore, mai shekaru 41 a duniya, shi da yaransa suna kula da wani yankin da ke bangaren Faskari, Kankara a Jihar Katsina da kuma wani yankin Zamfara.

Idi menore bai taba shiga sulhu ba. Shi cikakken Bafullatani ne dan asalin Katsina. Yana da mata da ‘ya’ya.

Majiyarmu ta ce ‘ya’ya da matansa suna zaune ne a wani gari a Arewa maso Yamma na kasar nan. Shi kadai da wasu ‘yan’uwansa suke zaune a daji.

Jaridar nan ta samu labarin cewa, mafi yawan yaran nan da aka dauka yanzu haka suna wani kauye mai suna MUTU da ke cikin Karamar Hukumar Gusau a Jihar Zamfara.

Mutu gari ne da ya dade a karkashin kulawar barayin daji. Wasu yaran kuma suna wani yanki na garin MADA; duk a cikin Karamar Hukumar Gusau a Jihar Zamfara.

A garin Kankara akwai sama da motocin soja 60 wadanda ga alama za a yi wa dajin kofar raggo ne, ba shiga, ba fita.

Majiyarmu ta tabbatar mana wasu daga cikin barayin dajin nan da ba da sanin su aka yi wannan mummunan aikin ba. Suna ba jami’an tsaro hadin kai. Suna kallon Awwalun Daudawa ya ja masu bala’in da ba su taba gani ba.

…’YA’YAN TALAKKAWA NE KAWAI A MAKARANTAR?

Ba kamar yadda aka dauka ba cewa makarantar zalla ‘ya’yan talakkawa ne, wannan ba haka ba ne, cikin yaran da ba a gani ba akwai ‘ya’yan manyan ‘yan boko da ‘ya’yan manyan masu rike da manyan mukamai a Jihar Katsina da kuma Tarayya, kamar yadda muka tabbatar da sunaye da mukamansu.
_______________________________________________
Jaridar Taskar Labarai na bisa yanar gizo www.taskarlabarai.com da kuma ‘yar’uwarta Katsina city News da ke a www.katsinacitynews.com da ta Turanci da ke www.thelinksnews.com. da sauran shafukan sada zumunta. Duk sako a aiko ga 07043777779.08057209539

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here