SATAR YARAN KANKARA:
KILA SHEKAU DA GASKE YAKE
Mu’azu Hassan
@ Jaridar Taskar Labarai
Binciken da jaridunmu suka yi, sun gano tana iya yiyuwa Shugaban Kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau da gaske yake cewa mutanensa na da hannu a satar daliban makarantar garin Kankara ta Jihar Katsina.
Bincikenmu a kan daya daga cikin wadanda ake zargin shi ne ya kitsa harin da kuma satar, mai suna Awwalun Daudawa, kila ya samo alaka da Boko Haram, ko dai ta akida, ko kuma ta kudi, ko amsar makamai, ko neman hadin gwiwa su yi aiki tare.
Bincikenmu a kan Awwalun Daudawa, wanda aka haifa a wani gari yammacin Kadisau ta Karamar Hukumar Faskari, daga baya ya koma wani bangare a Zamfara. Daga nan ya koma safarar makamai ga kungiyoyin yankin.
Bincikenmu ya gano Awwalun Daudawa, ya zauna wurare da dama a kan safararsa ta makamai da hulda da manyan ‘yan ta’adda.
Daga cikin inda ya zauna har da Jihar Yobe, wadda tana daya daga cikin matattarar ‘yan Boko Haram.
Awwalun Daudawa, ya horar da manyan yara wadanda an san su a kan rashin imani da tsara hare-haren ta addaci.
Wasu daga cikin yaransa sune Ibrahim Buji, wanda aka kashe a Birnin Gwari. Sai Ibrahim Nadanbu. An kashe shi ne a tsakanin Abuja da Kaduna.
Sauran yaran nasa sun hada Faura, Muwage da Bello Kurmin Doka. Wadannan su suna da rai.
Yaran Awwalun Daudawa suna masa biyayya, wanda ba sa kiran sunansa, sai dai Oga ko Jagaba ko Masta.
Wadanda muka tambaya game da shi sun ce, mutum ne mai son kiran Lamba, watau ya yi abin da zai jawo hankalin a kansa.
Awwalun Daudawa ya rika mai da hankali kan mummunan ayyukansa ne a yankin Neja, Birnin Gwari da tsakanin Kaduna da Abuja, kamar yadda bincikenmu ya gano mana.
Bincikenmu ya gano, Awwalun Daudawa ya raba daliban da suka sace ne ga wasu daga cikin barayin daji, wadanda ba za su yi iya jure matsi kamar yadda Boko Haram ke iyawa ba. Don haka akwai yiyuwar da yawan ‘yan fashin dajin su mika yaran nan ba tare da wata doguwar tirjiya ba.
Don haka wasu barayin dajin za su iya mika wuya a tattauna da su a kan yaran da aka ba su kaso, ba wai su jira sai Boko Haram ta ba su umurni ba. Don haka in an ce ana tattaunawa, tana iya zama gaskiya.
An dade ana zargin Boko Haram na neman samun wajen zama a wannan dajin, kuma duk masana da masu bincike sun san wannan.
Jaridar Taskar Labarai ta taba rubuta wata budaddiyar wasika ga hukumomin tsaro a ran 9 ga watan Afrilu, 2018 cewa, a farga fa. Wasikar ta samu yayatawa sosai a wasu kafofin watsa labarai.
______________________________________________
Taskar Labarai, jarida ce mai zaman kanta da ke bisa yanar gizo www.taskarlabarai.com.tana yar uwa ta Turanci mai suna The Links News.www.thelinksnews.com.da kuma katsina city news.@ www.katsinacitynews.com. Duk sako a aiko ga 07043777779.email Newslinks@gmail.com.ko katsinaoffice@yahoo.com